Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya amsa cewa dole ne tawagarsa ta sake lale, tare da ƙara ƙaimi a kan yadda ta ke tsaron baya, dai dai lokacin da ƙungiyar wadda ta ƙarƙare a matsayin ta biyu a kakar da ta gabata, ga fama da rashin nasara a wannan kaka.
Liverpool wadda yanzu haka ke matsayin ta 9 a teburin gasar Firimiya, bayan nasara a wasanni 2 kacal daga cikin 7 da ta doka a wannan kaka.
Ƙungiyar dai na ci gaba da shan caccaka musamman daga magoya baya, ganin yadda ta yi sake har ƙwallaye 14 suka shiga ragarsu a wasanni 9 da suka buga a wannan kaka, wanda ke nuna cewa a wasanni biyu ne kawai suka iya hana ƙwallo taba zarensu ba.
Ko a wasansu na ƙarshen mako, Liverpool ta bari ƙwallaye har 3 sun shiga ragarsu inda suka tashi ƙwallaye 3 da 3 a karawarsu da Brighton ranar Asabar, lamarin da ya sa yanzu Arsenal da ke a matsayi na 1 ta ba su ratar maki 11, Manchester City da ke matsayin ta 2 kuma ta ba su ratar 10.
A cewar Jurgen Klopp wajibi ne su zage damtse don fita daga matsalar da suke fuskanta, wanda a cewar kocin na da nasaba da rashin tsaro a baya.