Ronaldo na da damar tafiya a duk lokacin da ya so – Man United

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ce ta na a shirye idan har Cristiano Ronaldo zai sake jarraba barin ƙungiyar a watan Janairu, idan har ɗan wasan gaban ya gaza samun wuri a tawagar Erik Ten Hag, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

Ronaldo mai shekaru 37 ya yi zaman benci a wasan da Man United suka sha kashi 6-3 a hannun Man City a wasan hamayya da suka gwabza a gasar Firmiyar Ingila a ƙarshen makon da ya wuce, haka zalika bai fara a wasan da suka yi rashin nasara 4-0 a hannun Brentford ba.

Ya ƙagara ya bar Old Trafford a wanna kaka amma abin ya ci tura, kuma United sun kwana da sanin cewa yana iya neman tafiya a watan Janairu a ƙoƙarin da ya ke ne neman buga wasa a kullum.

Ronaldo ya ci ƙwallo 1 ne kawai a wasanni 8 da ya buga, kuma yanzu haka yana bayan ‘yan wasan gaba irin su Marcus Rashford da Antony Martial a tawagar Manchester United.