Akwai sauran mutanen jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a daji

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Za a ji ana sako fasinjojin da ɓarayi su ka sace a harin jirgin ƙasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tun ranar 28 ga watan Maris ɗin bana 2022 miladiyya, amma har yanzu akwai sauran mutane da ke dajin cikin matuƙar takaici da rashin sanin tabbas. Duk haka su din ma masu nisan kwana ne don lokacin mummunan farmakin fasinjoji 9 su ka gamu da ajali. A wannan lokacin ko ma rai bai yi halin sa ba, ko ba a sace mutum ba, akwai mummunan tashin hankali na rugugin harbin bindiga da firgita marar misali.

Waɗanda su ka tsira a lokacin harin sun ba da labarin yadda lamarin ya afku da ban tsoro da juyayi. Akwai wanda ya buya ƙarƙashin wanda a ka harbe ya yi shiru tamkar shi ma ya mutu. Ya zama mai muhimmanci mu cigaba da addu’ar neman kariyar Allah daga fuskantar irin wannan yanayi da za a daɗe a rayuwa ba a manta da shi ba. A na ta murna an samu hanya mafi tsaro ta hanyar shiga jirgin ƙasa a tsakanin muhimman biranen biyu, sai ga shi kwatam wasu sun haddasa cikas ga wannan hanya.

Gabanin afkuwar akasin mutane kan kwantar da hankali in su na cikin jirgin ƙasan don ba ya ga kasancewar sa a rufe kirib kuma ba a ko ina ya kan tsaya ba, hakanan a kowane taragu akwai jami’an tsaro. Har nasiha a ke yi wa mutane da cewa duk lokacin da su ka shirya tafiya tsakanin biranen biyu su shiga jirgin ƙasa don yadda ya ke da tsaro. Farkon fara jigilar ma hatta manyan jami’an tsaron ƙasa da gaggan ’yan siyasa kan jingine motocin su, su shiga jirgin. A jirgin akwai gefen masu hannu da shuni da rahoto ya bayyana lokacin da maharani su ka zo sun fi maida hankali kan wannan taragu.

Irin labarin miliyoyin kuɗin da a ke ambatawa a na karɓa kafin sako fasinjojin na nuna miyagun sun shirya tsaf da sace wasu daga waɗanda su ke tunanin na da maƙudan kuɗi. Gaskiya ba za a ce lalle don an ga mutum a taragun manyan mutane ke nuna mai kuɗi ba ne, don wani zai iya shiga ajin masu kuɗin alhali ba shi da kuɗin. Na tava samun labarin yadda wasu kan yi wuf su faɗa jirgin ba tare da sun sayi tikiti don dalilin wa imma ba su da kuɗin, ko sun makara har jirgin na daf da tashi don haka jira sai har an sayi tikiti kan iya sa su rasa shiga jirgin don haka ko su fasa tafiya ko kuma su rungumi ƙaddarar shiga mota su bi hanyar mai hatsari.

Yadda maharani su ka tinkaro jirgin da muggan makamai, ga shi kuma su na da yawan gaske ya sa jami’an tsaron rakiya ba za su iya kare jirgin ba. A irin wannan yanayi in jami’in tsaro ya yi dabarun tserar da kan sa ma ya yi ƙoƙari. Na ji ma a na hirar wani babban jami’in tsaro ya rarrafa ya koma taragun talakawa don tsira daga miyagun. Hakanan an samu wani bawan Allah da ya sha alwashin ba zai bi varayin ba, sai dai su yi ma sa abun da su ka ga dama. Haka miyagun marasa Imani su ka harbe shi. Bawan Allan na daga hotunan farko da su ka fito na marigaya daga jirgin.

Wannan ya yi kama da yanda mutum zai zavi sadaukar da rayuwarsa in yaqi ya same shi har gida. Maimakon kaskanci gara mutum ya taɓuka kuma in da sauran shan ruwa sai ka ga Allah ya tserar da mutum. Ba don muhimmancin bin wannan hanya ba don kasancewar ta ƙofar jihohin arewa maso yamma 7, da mutane sun dakatar da bin hanyar har sai an samu sararawar hare-haren nan.

Waɗanda su ka bi hanyar a ’yan kwanakin nan na cewa an baza jami’an tsaro da ke sintiri don kare lafiyar jama’a. Duk da haka za ka ga hotunan bidiyo da ke nuna ɓarayin na nan su kan fito inda jami’an kan yi ƙoƙarin magance su ko korar su, su koma daji don mutane su samu su cigaba da tafiyarsu. A irin haka za ka ga tambayoyi na yawa cewa a ainihin ina ne a dajin nan ɓarayin kan zauna? Shin cikin duhuwa su kan shiga ko kogon dutse?

Na taɓa samun wani mai sarauta daga ɗaya daga fitattun ƙauyukan da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna wanda ya ce sam miyagun ba sa samun mafaka a garin su. Ya nuna duk mai tunanin akwai ɓarayin a ƙauyukan da ke baƙin babban titin ya sauya tunani don ba a nan su ke zama ba. Lokacin da a ka kawo tunanin miyagun kan iya fakewa a ƙauyukan, wasu sun ba da shawarar a kafa barikokin soja a tsakanin ƙauyukan ko ma a tada wasu ƙauyukan ya zama ba inda wani mai mugun nufi zai iya buya ko samun abun masarufi da gaggawa.

Ni ina ganin abun da zai zama mafi a’ala a nan shi ne jami’an su riƙa hulɗa da mutanen ƙauyukan don samun bayanan sirri. Na tabbata ma jami’an na yin hakan don ƙwarewar aikinsu ya nuna hakan na daga fitattun hanyoyin yaƙar miyagu. Ban ji labarin da ke nuna ko ɓarayin na tava mutanen ƙauyukan ko kuma su na zaman kowa ya yi harkarsa.

In an kawar da wannan tunani, za a fahimci zai yiwu mutan ƙauyukan na cikin tashin hankali don maƙwabtaka da mugu ba alheri ba ne. Wani abun dubawa shi ne masu ƙasa kaya a gefen ƙauyukan don sayarwa ba lalle ba ne su riqa samun ciniki kamar yanda su ke yi gabanin wannan yanayi na taɓarɓarewar tsaro. Duk inda ya zama ba kwanciyar hankali, to ba shakka tattalin arziki ma na cikin garari. Waɗanda kan shiga mota su bi hanyar bas a sha’awar tsayawa, kuma in sun ma tsayan ba sa fatan su ɓata lokaci. Tsayawar da mutane kan yi na raya wasu sassa da kan zama tamkar kasuwanni. Akwai inda masu bin mota kan tsaya su ci abinci ko in Musulmi ne su yi sallah.

In mun koma kan hari kan jirgin ƙasan na watan Maris, barayin daji masu shigen ’yan Boko Haram sun sake ƙarin mutum 5 daga cikin waɗanda su ka ɗauke a sanadiyyar harin da su ka kai kan jirgin ƙasa da ke tafiya tsakanin Abuja da Kaduna.

Sakin ya biyo bayan wasu mutum 4 da varayin su ka sake makwan jiya da su ka haɗa da wani lauya wanda ya yi jawabi a faifan bidiyon da ɓarayin su ka sake don ƙona zuciyar gwamnati. Lauyan ya tsaya ya yi kira ga hukumomin qasa da ƙasa su kawo mu su ɗauki. A zahiri za a fahimci miyagun na son tunzura gwamnatin Nijeriya ne ta biya mu su bukata tun da ga shi waɗanda su ka kama na kira ga manyan ƙasashen duniya su sa baki a lamarin.

Sabbin waɗanda a ka saken sun haɗa da malami a jami’ar Usman Ɗanfido a Sakkwato, Mustapha Imam.

Sauran sun haɗa da Akibu Lawal, Muktar Shu’aibu, Sidi Sharif da Abubakar Rufai.

Ba a samu wani ƙarin bayani ba ko ’yan uwan mutanen da su ka samu kan su, sun biya mu su kuɗin fansa ko kuwa a’a. Mai shiga tsakani Malam Tukur Mamu ya baiyana irin hakan lokacin da a ka saki mutanen na baya cewa ba a tantance haƙaƙanin an ba da kuɗi ne gabanin sako mutanen ba. Mamu wanda muƙarrabin Dr.Ahmad Gumi ne ya ce ya janye kansa daga shiga tsakani na neman sako sauran mutanen. Mamu wanda shi ne mawallafin jaridar DESERT HERALD ya bayyana cewa a na yi ma sa barazana kan wannan aikin da ya ke yi don haka ya janye kansa. Duk da haka waɗanda a ka sakon sun ziyarce shi kuma an ga sun dauki hoto tare ya na tsakiyar su.

Har yanzu akwai sauran mutum 34 maza da mata a hannun ɓarayin da ke barzanar ɗanɗana mu su azaba ta hanyar duka da bulala.

Kammalawa;

Taɓarɓarewar tsaro a sassan Nijeriya na ƙara firgita jama’a don yadda ba wanda ya tsira tsakanin fararen hula a kan titi da su kan su jami’an tsaron.

Labarin ɗaukar ƙarin matakan tsaro a cikin Abuja da Kano na daga lamuran da ke ƙara nuna ba a samu bakin zaren warware ƙalubalen tsaron ba.

Duk da ya ke dama duk a shekarar zaɓe ko yaƙin neman zaɓe a kan iya samun irin wannan barazana da kan hana mutane sukuni.

Rashin tsaron ya sa mutane na zama cikin takatsantsan da kuma yin addu’ar neman kariya daga Allah.

Shugaba amintattu na gamaiyar ƙungiyoyin Arewa Nastura Ashir Sharif ya ce gwamnatin na bayyana cewa ta na ware maƙudan kuɗi kan tsaro amma kamar ba a gani a ƙasa.

Fadar Aso Rock dai kan ce a riƙa fidda siyasa a lamuran tsaro don har dai za a cimma nasara kan samar da tsaro sai kawo ya ba da haɗin kai.

Lokaci-lokaci za ka ga an raba lambobin gaggawa na tuntuɓar jami’an tsaro don bugawa da zarar an ga abun da ba a amince da shi ba.

Shin lambobin su na amfani ko kuwa a’a, ingantar tsaron ko akasin haka zai zama amsa.