A yayin da Tarayyar Nijeriya ke ci gaba da fuskantar barazanar ambaliya ruwa a sassa dabam-dabam, gwamnatin ƙasar ta ce ba ta da haufin ingancin madatsun ruwan da Nijeriyar ke da su.
Kama daga tituna da gadoji da ma uwa uba gidajen al’umma dai, sannu a hankali ambaliyar ruwa na bazuwa a sassan Tarayyar Nijeriyar dabam-dabam. Kuma ya zuwa yanzu, kimanin jihohi 28 da ƙananan hukumomi 121 ne ambaliyar da ke yin barazana ta shafa a ƙasar. An fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni a tarihin Nijeriya a shekarar 2012, inda aka yi asarar kusan dala biliyan 16.9.
Daga cikin manufofin ci gaba mai ɗorewa guda 17 don samun ci gaban bil’adama nan da shekarar 2030 kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana, fiye da rabin waɗannan manufofin na iya fuskantar barazana kai tsaye ta hanyar ambaliya.
Misali, ambaliya na iya shafar samar da tsaftataccen ruwa da tsaftar muhalli, da kuma kawar da fatara da yunwa. Saboda haka, ambaliya tana nuna barazana ga ɗorewa ganin cewa zai iya shafar lafiya, rayuwar jama’a, muhalli da tattalin arziki marar iyaka.
Abubuwan da ke haifar da ambaliya a Nijeriya galibi suna faruwa ne a dalilin rashin sanin yadda ya kamata a tafiyar da yanayin. Wasu lokuta wuraren zama da yawa suna da ƙarancin magudanan ruwa, wanda ya kamata a samu isassun magudanar ruwa don wucewan ruwan saman cikin sauƙi. Yayin da biranen ke ƙaruwa, hakan na nufin cewa yanayin muhalli ya canja zuwa babban matsayi ta yadda waɗanda aka gina a da ba za su iya ishen ruwan ba.
Wani abin da ke janyo ambaliya a Nijeriya yana da alaƙa da rashin kula da shara, musamman sharar gida. Ɗabi’ar da jama’a ke da shi game da zubar da shara da kuma rashin ingantaccen aikin kawar da sharar, musamman a ƙananan birane da ƙauyuka shi ne babban abin da ke haifar da ambaliya. Waɗannan shara-sharar sun kan toshe manyan magudanan ruwa hatta a mafi yawan biranen ƙasar.
Bugu da ƙari, rashin bin ƙa’ida wajen faɗaɗa magudanan saboda ƙaruwar yawan jama’a da kuma ƙaura daga ƙauyuka da qananan birane yana haifar da rashin ingantattun ababen more rayuwa. Har ila yau, yankunan noma suna ƙara rikiɗa zuwa wuraren zama don magance havakar giɓin gidaje, ba tare da shirin da ya dace ba.
Rashin gaskiya, rashin amimci da yadda wasu jami’an tsare-tsaren muhalli ke gudanar da ayyukansu kuma yana haifar da matsalar, inda su ke yin abin da suka ga dama ba tare da bin tsare-tsaren da aka amince da su. Waɗannan ɗabi’un suna jefa wasu mutane cikin matsala inda sukan yi gini mara inganci ta hanyar shimfiɗa tsarinsu a wuraren da ba a yarda da su ba, kamar kafa gine-gine a kan magudanar ruwa.
A kwanakin baya ne Babban Daraktan Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet), Farfesa Mansur Matazu ya shawarci ’yan Nijeriya musamman mazauna Taraba da wasu yankunan kudu maso yammacin ƙasar da su yi shiri domin fuskantar ambaliya sakamakon hasashen damina.
A cewar Farfesa Matazu, NiMet sun sami daidaiton kashi 95 cikin 100 a hasashensu cikin shekaru 15 da suka gabata.
Ya ƙara da nuna damuwarsa kan yadda wasu jihohi da ƙananan hukumomi ba sa bin gargaɗin farko da gwamnati ta yi ta hanyar yin daidai da ayyuka a matakin ƙasa da ke da nufin daƙile illolin ambaliyar ruwa. Ya kuma bayyana buƙatar ma’aikatu da Hukumomi (MDAs) su yi la’akari da duk gargaɗin da NiMet ke bayarwa don rage tasirin ambaliya.
Hukumar ta yi hasashen cewa a wasu sassan Nijeriya za a samu ruwan sama fiye da yadda aka saba da ma ambaliyar ruwa.
Tuni dai aka samu rahoton ambaliyar ta fara ɓarna, inda a wasu wurare ta mamaye gine-gine, ko ta share hanyoyin mota, ko ta tafi da gonaki, ko ma ta yi sanadin mutuwar mutane.
Baya ga matakan da ake ɗauka a halin yanzu dangane da tsarin gargaɗi da rage raɗaɗi, akwai sauran ƙalubale da ya kamata a shawo kan su. Misali, manufar magance ambaliyar ruwa a Nijeriya. Hakan na nufin akwai giɓi ta fuskar tsare-tsaren doka da tsare-tsare masu dacewa don shawo kan matsalar ambaliyar ruwa a Nijeriya. Wani misali na abin da za a iya yi shi ne, a riƙa sanya ido kan ambaliyar ruwa a matsayin muhimmin sashi na ayyukanmu na tsara birane da yanki.
Bincike ya nuna cewa, a tarihi Nijeriya ta fi karkata kan mayar da martani bayan ambaliya fiye da maganceta kafin faruwarta. Don haka, gwamnati za ta iya ba da fifiko ga fuskantar haɗarin ambaliya a matsayin wani vangare na tsarin kula da haɗarin bala’o’i a ƙasar. Don cimma wannan, gwamnati na iya ɗaukar darasi daga rahoton tantance haɗarin da aka yi a Nijeriya a shekarar 2012 tare da taimakon masu haɗin gwiwa na cikin gida.
Dukkanin fasahar da ake buƙata don cimma waɗannan za a iya samo su daga cikin Nijeriya. Bugu da ƙari, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) za ta iya amfani da tsarin bayanai na ‘Geographic Information System’ (GIS) don samar da sahihan bayanai na ambaliyar ruwa a cikin ƙasar. Haka kuma yana da kyau a samar da ingantattun tsare-tsare na gargaɗin farko na ƙasa domin faɗakar da ’yan Nijeriya kan duk wata ambaliyar ruwa da ke tafe a matakin ƙananan hukumomi, jihohi da tarayya.
Kamar yadda MDA ke ba da hasashen yanayin ruwan sama, ya dace daidai da inganta hanyoyin sadarwarsu a tsakanin MDA, da na waje tsakanin MDA da ’yan Nijeriya. Don inganta ayyuka masu ɗorewa, ya kamata a ƙarfafa abubuwan more rayuwa masu jure wa yanayi a duk faɗin ƙasar. Wannan kuma ya kamata ya haɗa da matakan tsari kamar ɗaga tsayin gine-gine don yin la’akari da hauhawar matakin ruwa ko amfani da abubuwan more rayuwa kamar kariya ko haɓaka tsarin magudanar ruwa.
Mu a Blueprint Manhaja mun yi imanin cewa idan aka ɗauki waɗannan matakai, za a magance matsalolin da ke haifar da ambaliyar ruwa yadda ya kamata a matsayin hanyar da Nijeriya za ta iya cimma burin ci gaba mai ɗorewa.