Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi sun kama wani ma’aikacin gidan gyaran hali, Ibrahim Abubakar Ka’oje bisa ga zargin hannu a cikin wata sata da aka yi a gidan Hajiya Rabi da ke garin Ka’oje a ƙaramar Hukumar Bagudo a jihar Kebbi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sufurtanda Nafi’u Abubakar ya bayyana cewa an samu nasarar kama wannan jami’in ne bayan da Hajiya Rabi ta kai rahoton waɗansu mutane sun haura ta gidan ta a garin Ka’oje inda su kuma ‘yan sandan ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka kamo shi, bayan bincika mai zurfi ya tabbatar da yana da hannu a cikin satar kuma tuni an sayar da waɗansu kayan ga Sa’adu Ibrahim Darhami, Hamza Ahmad da suke zaune a jihar Sokoto, sai kuma Nasiru Sani da Tasi’u Umar Zauro, da ke zaune a Birnin Kebbi.
Ya ƙara da cewa a cikin binciken an gano abin hannu guda biyu da babur ƙirar Haojeu da wata ƙirar Iphone 16 Samsung Galaɗy da kuma Samsung Flip.
Har wa yau dai binciken ya nuna akwai Ibrahim Usman Oroji wanda shi ne ya taimaka wajen sayar da waɗansu daga cikin kayan wanda ya cire wa kan sa Naira miliyan biyu da rabi a matsayin nasa kaso.
Yanzu haka dai rundunar ta baza komar ta don farauto sauran waɗanda ke da hannu a cikin wannan aika-aikar tare da ɗaukar matakin da ya dace.
