Dalilin da ya sa ban damu da neman wa’adi na biyu ba – Gwamnan Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce, mulkin siyasa Allah ne kawai ya ke bayar da shi, kuma Shi ke ɗora shugabanni da sauke su daga kan mulki bisa ga nufinSa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa kuma darakta janar na yaɗa labaran fadar gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Da yake yin tsokaci kan ƙalubalen da ya fuskanta bayan zaɓen 2023, Gwamna Yusuf ya ce, ya jure lokaci mafi wahala a rayuwarsa, amma ya ci gaba da jajircewa wajen yi wa al’ummar Kano hidima.

“Na fuskanci ƙalubale mafi tsanani a rayuwata bayan zaɓen 2023. Amma ta waɗannan ƙalubale da hawaye, na ci gaba da jajircewa wajen yi wa Kano hidima, har yanzu Ina yi saboda Allah, ba don wani mutum ba,” inji shi.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa, shugabanci ba ya hannun wani mutum. Ya ƙara da cewa, “Allah ne ke naɗa shugabanni da tsige shugabanni a duk sanda ya so.”

A kan makomar siyasarsa, gwamnan ya bayyana cewa, neman sake tsaya wa takara shine na biyu a aikin da yake yi na mulki a halin yanzu.

“Ko na sake neman takara ko ban sake tsaya wa takara ba, aikina shine na ci gaba da gabatar da shirye-shirye masu ma’ana da za su amfanar da jama’a, na san cewa wata rana zan bar wannan kujera, shi ya sa nake yin iyakacin ƙoƙarina a yanzu don kawo sauyi a Kano a zahiri, zamantakewa, da ɗabi’u,” inji shi.

Gwamna Yusuf ya jaddada ƙudirinsa na tinkarar ƙalubale a harkokin mulki. “ƙalubale na iya zuwa, hawaye na iya zubowa, amma ƙudurin da na ɗauka na kawo sauyi a Kano ya fi ƙarfi fiye da kowane lokaci,” inji shi.

By ukarofi