Daga BASHIR ISAH
‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zaɓi Rt. Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi (APC- Umaisha/Ugya) a matsayin Shugaban Majalisar jihar ta bakwai.
Kazalika, ‘yan majalisar sun sun zaɓi Hon Abel Yakubu Bala (PDP- Nassarawa Eggon ta Yamma) a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.
Muƙaddashin akawun majalisar, Hon Ibrahim Musa, shi ne ya sanar da hakan yayin rantsar da mambobin majalisar ta bakwai a Lafia, babban birnin jihar.
Akawun majalisar ya ce an rantsar da mambobin majalisar ne daidai da damar da Gwamnan Abdullahi Sule na jihar ya bayar wanda ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa.