Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Idan ba a manta ba jaridar Blueprint Manhaja a kwanan nan ne ta kawo muku labarin rigimar da ta ɓarke akan zaɓen sabon shugabancin majalisar dokokin jihar ta Nasarawa karo na 7, inda a ƙarshe aka samu ɓangarori 2 wato ɓangaren Honorabul Oga Ogazi da na shugaban majalisar dokokin dake neman zarcewa wato Honorabul Balarabe Ibrahim Abdullahi.
Kasancewa rigimar ya ƙi ci ya kuma qi cinyewa ne sai wasu masu ruwa da tsakin jihar dake faɗa aji da sarakunan gargajiyan jihar da sauran su ciki har da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule suka ɗauki ƙwararren mataki a karon nan don kawo ƙarshen rashin jituwar wato tabbatar an samu dunƙulalliyar majalisa dake da shugaba ɗaya tilo kamar yadda ake da su a sauran jihohin ƙasar nan.
Sai dai hakan bai haifar da ɗa mai ido ba kasancewa a ƙarshen taron wanda aka gudanar a wajen jihar wato a gidan baƙi na gwamnan jihar dake Asokoro Abuja wato Governor’s Lodge, an tashi baram-baram ne wato kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, inda aka kasa cimma burin haɗa kawunan ‘yan takarar 2.
Kodayake an gudanar da taron ne cikin sirri ta bayan fage ba a yarda manema labarai sun shiga cikin ɗakin taron ba amma jim kaɗan bayan taron manema labaran ciki har da wakilin mu a jihar sun gano cewa ba a cimma burin haɗa kawunan ɓangarorin biyu ba.
‘Yan jaridan sun samu damar tattaunawa da wasu na kusa da ‘yan takarar musamman daga ɓangaren Oga Ogazi da suka buƙaci a sakaya sunayen su inda duk suka tabbatar musu cewa an tashi taron ne ba tare da cimma matsaya ko haɗa kan ‘yan takarar su zama ɗaya ba.
Kodayake bayan taron babu wanda ya gana da ‘yan jarida cikin ‘yan takarar da mambobinsu dangane da sakamakon taron kamar yadda aka saba ba.
Sai dai binciken ya tabbatar da hakan, kuma binciken ya gano cewa kammala taron ke da wuya sai kowa ya kama gabansa ba tare da vata lokaci ba aka koma gida wasu a daren ta ranar Talatar mako da ake ciki, wasu kuma washegarin.
Yanzu dai al’ummar jihar da ƙasa bakiɗaya na cigaba da zura ido ne su ga yadda za a warware matsalar a samu dunƙulalliyar majalisa mai kuma shugaba guda ɗaya duk da a yanzu haka an amince ne da ɓangaren Balarabe Abdullahi a matsayin ainihin kakakin majalisar dokokin wanda ita ma gwamnatin jihar kanta ke hulɗa da shi a hukumance da sauran hukumomi a jihar.