An yi jana’izar Sheikh Yusuf Ali a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Sheikh Dokta Yusuf Ali rasuwa.

Sheikh Dokta Yusuf wanda shi ne Sarkin Malaman Gaya ya rasu ne a daren Lahadi bayan ’yar gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 73.

Ɗan marigayin, wanda ɗan siyasa ne, Muslihu Yusuf Ali ya shaida wa Blueprint Manhaja cewa, an yi janaizar mahaifin nasa a ranar Litinin da Azahar a Masallacin Murtala da ke kusa da titin Gidan Zoo.

Shehin malamin ya gudanar da rayuwarsa ta aikin gwamnati a matsayin alƙali, inda ya jagorancin kotunan Shari’ar Musulunci daban-daban a Jihar Kano, kafin ya yi ritaya a shekarar 2009.

Bayan koyarwar addini da ya ɗauki tsawon lokaci yana yi, malamin ya yi tashe wajen taimaka wa al’umma ta fuskar cututtuka daban-daban ko kuma ma dai shafar aljanu.

Shehin malamin ya rasu ya bar ‘ya’ya 38 da jikoki da dama.

Da yake aike da saqon ta’aziyyarsa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngalale, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini rashin babban malamin, inda ya miƙo saƙon ta’aziyyar ga iyalai, ɗalibai, da kuma mabiya malamin da ke Kano, da ma Masarautar Gaya.

Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abin alhinin da ya karaɗe muryoyin jama’a a faɗin ƙasar nan, duba da irin ɗimbin mabiyan da marigayin ke da shi musamman ma mabiyan Ɗarikar Tijjaniyya a ciki da wajen Nijeriya.

Haka zalika Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin da kuma gwamnatin Jihar Kano da al’ummar jihar da ma ɗaukacin Musulmin Nijeriya bisa wannan rashi da aka yi, ya na mai addu’ar Allah ya jiƙan malamin.