An yi wa Shugaban Ƙasa da gwamnoni ƙarin albashi da kashi 114

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tattara da Raba Kuɗaɗen Shiga (RMAFC), ta amince da ƙarin albashi da kashi 114 ga manyan jami’an gwamnati.

Waɗanda ƙarin albashin ya shafa sun haɗa da Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa, gwamnoni, ‘yan majalisu, ma’aikatan shari’a da sauransu.

RMAFC ita ce hukumar da ke tantance albashin da ake yanka wa ‘yan siyasa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, ciki har da Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da sauransu kamar yadda Sashe na 84 da 124 na Kundin Tsarin Mulki ya nuna.

Shugaban RMAFC, Muhammadu Shehu, bisa wakilcin kwamishina a hukumar, Rakiya Tanko-Ayuba, shi ne ya bayyana haka yayin gabatar da rahoto ga Gwamnan Kebbi, Dr Nasir Idris, ranar Talata a Birnin Kebbi.

Ya ce ƙarin albashin ya fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairu 2023.

Ya ƙara da cewa, matakin ƙarin albashin ya yi daidai da tanadin doka sakin layi na 32(d) na kashi na 1 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.