Aure: Dankali sha kushe?

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN

Ni dai na fahimci kamar akwai kamfen da aka ɗauko na yaƙi da aure a Arewa, kuma ana bin hanyoyi da dama wajen ƙoƙarin ganin aure ya zama abin ƙyama da ban tsoro ga al’ummarmu.

Masu yin wannan kamfen ɗin ma ba lallai ba ne su san kamfen suke ba, ƙila ma hankalinsu bai kai nan ba.

A kullum in ka shiga “group” na arewa, da ke tattauna matsalar zamantakewa, za ka lura cewa an fi kawo matsalar aure, kullum ƙorafi ake a kan matsalar aure, da kawo labarai na rashin mutunci da ta da hankali a kan ma’aurata. Abin haushin za ka lura suma masu waɗannan “shafukan” ba wata shawara suke kawowa ba ta ilimi, kawai “screen shots” suke a su turawa mabiya “shafukan” ko “Guruf” ɗinsu ai ta “comments” na molonka.

A irin haka, an zarewa maza da mata (musamman mata) son yin aure, an tsorota su, an nuna musu cewa aure wahala ne, masifa da bala’i ne, sannan wani fagen daga ne da ake gwabza yaqi tsakanin mutane, har ta kai yanzu akwai mutanen da suke ganin gwamma su yi zamansu ma ba auren.

Wata hanyar da ake bi wajen yaɗa kamfen ɗin ƙin aure, ita ce sai a samu wata gogaggiya mara aure, ta dunga bayyana cewa ai aure bauta ce, wahala ce, sannan yana daƙile cikar burin ‘ya mace na yin karatu, ko na yin sana’a da sauransu.

qiri-qiri sai ai ta qoqarin bayyana cewa aure matsalarsa ta kai in har mace tana da shi ba abin da za ta tsinana a rayuwa, wanda mu ko mun san ba haka ba ne, akwai wanda aure ne ya kai su, su ka cimma burinsu a rayuwa, sun fi ma yawa nesa ba kusa ba.

Amma in har mu ka tafi a haka, to mun ɗauko hanyar rayuwar Turai da Amurka, kullum aure baya ya ke a ƙasashensu, wai saboda wahalarsa da ɗawainiyarsa, don haka, fasadi da ‘ya’yan shegu su ke ta yawaita, sabbin hanyoyin manyan saqo ke haɓaka.

Yanzu da aure da zama haka ga baligi ko baliga wanne ya fi? (Ba ina magana ba ne, a kan wanda suna son aure, kuma Allah bai kawo lokaci ba, wannan mutanen kirki ne, Allah ya kawo mu ku abokan zama salihai, su zam muku sanyin idaniya).

Sannan kowa ka gani tutiya ya ke da iyayensa, da su ka yi silar zuwansa duniya ta hanyar aure, kenan abu ne mai daraja? Wa zai alfahari da shi shege ne?

Na yarda cewa akwai cikin maza da mata masu wofantar da haƙƙin aure, amma tsangwamar shi auren ne mafita? A’a sam ba zai tava zama mafita ba, mafita shi ne a kalli harkar aure a Arewa, sannan a bi dokokinsa da haƙƙoƙinsa, hukuma ta shigo ciki, sannan ai ta wayarwa da mutane kai a kan aure, a buɗe makarantun koyar da aure, a ƙarfafe su.

Allah ya sakawa Farfesa Umar Sani Fagge da alheri, ya buɗe makarantar koyar da aure ta maza kacokan, duk dai don a fahimci aure a san darajarsa. Akwai ire-irensu ma nan da can. Irin haka muke son gani, wato a bi hanyar gyara ba hanyar ɓaɓatu da kushe aure ba.

Mukhtar Sipikin, ɗan siyasa, marubuci kuma mai sharhi a kan lamurran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.