Barazanar rashin ɗaukar mataki a kan tava janibin Annabi (SAW)

Daga ABDULAZIZ T. BAƘO

I yanzu dai ina ga ya kamata a ce mahukunta sun gane cewa rashin daukar mataki a kan waɗanda suke tava martabar Annabi (s.a.w) ba ƙaramar barazana ba ce ba ga zaman lafiyarmu. Domin kuwa muddin za a ci gaba a haka, toh mutane za su ci gaba da daukar doka a hannunsu. Shi kuma ɗaukar doka a hannu babbar barazana ce ga zaman lafiyar al’umma.

Kullum ina faɗa, ya kamata musulmi su rika zama masu jajircewa wurin tsayawa tsayin daka akan kare abinda suke so su ga an yi ba tare da balla doka ba. Wannan hanya ita ce hanya mafi inganci wurin raya al’umma. Komai kyawun manufarka in dai sai ka ɓalla doka za ka cim mata, to zai yi wahala ka cimma nasara.

Yanzu waɗannan samari na Sokoto an kama su. Ba ni da haufi akan cewa CAN za ta tsaya tsayin daka ta bibiyi hukuncin da za a yi musu, Za kuma su tabbatar cewa an biya diyyar ran wacce aka kashe kamar yadda aka yi a Kano shekarun baya. Kuma duk za su cimma waɗannan abubuwan ne bisa bin doka da tsari.

Mu fa? Mun fi son abu sha yanzu, magani yanzu. Ba za mu iya jajircewa mu bi kadin abubuwa ba. Ina kes ɗin waɗanda aka kama a baya da laifin tava martabar Annabi (s.a.w)? A wane hali kes ɗin su yake ciki yanzu? Ina waɗanda suka kashe Janar Alkali? A wanne hali suke yanzu?

Me ya sa gaba ɗayanmu ba za mu yi amfani da wannan harzuƙar da muka yi ba wurin ganin cewa mun bi kadin waɗannan kesa-kesan. Sau nawa kes din tava martabar Annabi (s.a.w) ya tavaa zuwa kotun ƙoli? Wane hukunci kotun ƙolin ta yanke?

Yan siyasar nan mu muke zavar su. Abinda muke so dolensu shi za su yi mana. Menene dalilin da ya sa ba za mu haɗa murya ɗaya mu ce musu muna so mu ga an zartar da hukunci ga wadannan mutane ba? In dai da gaske muke son Annabi (s.a.w), me zai hana duk wata ƙauna da muke wa yan siyasan mu ajiye ta mu ce buƙata ɗaya ce muke da ita gare su shi ne, kafin su sauka daga muƙaminsu, kes ɗin waɗannan mutanen ya shiga mataki na gaba. Idan bai shiga mataki na gaba ba ba za mu sake zaɓarsu ba?

Ko kawai soyayyar tamu a iya zage-zage da tsine-tsine ta tsaya?

Abdulaziz T. Bako, mai sharhi ne a kan lamurran yau da kullum. Ɗan Nijeriya ne mazaunin ƙasar waje.