Editor

9513 Posts
Yajin aikin gargaɗi: NLC ta ƙaurace wa zaman sulhu da Gwamnatin Tarayya

Yajin aikin gargaɗi: NLC ta ƙaurace wa zaman sulhu da Gwamnatin Tarayya

Shugabanni ƙwagiyar ƙwadagobta ƙasa (NLC) sun ƙaurace wa taron Ministan Ƙwadago, Simon Lalong, da zummar daƙile yajin aikin gargadi na yini biyun da ƙungiyar ta ƙuduri aniyar farawa. Majiyarmu ta shugabannin ƙungiyar 'yan kasuwa (TUC), Festus Osifo ne kaɗai aka gani a wajen taron wanda aka fara da misalin ƙarfe 5:52 na yammacin ranar Litinin. A ranar Juma'a NLC ta bayyana aniyyarta ta fara yajin aiki na kwana biyu a faɗin ƙasa daga ranar Talata, 5 ga Satumba, a matsayin gargaɗi ga gwamnatin tarayya. NLC ta ce ta ɗauki matakin yin yajin aikin ne domin nuna wa duniya rashin jin…
Read More
An rantsar da Janar Nguema shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya a Gabon

An rantsar da Janar Nguema shugaban ƙasa na riƙon ƙwarya a Gabon

A ranar Ltinin aka rantsar da Janar ɗinda ya jagoranci juyin mulki a ƙasar Gabon, Brice Oligui Nguema, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya bayan hamɓarar da Shugaba Bongo. Janar Nguema, ya jagoranci juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Larabar da ta gabata kan shugaban ƙasar Ali Bongo Ondimba, wanda ya fito daga gidan iyalan da suka mulki ƙasar sama da shekaru hamsin. Sojoji sun kifar da gwamnatin Bongo ne bayan da aka bayyana na shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a watan da ya gabata bayan da ‘yan adawa suka…
Read More
Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari’ar zaɓen shugaban ƙasa

Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari’ar zaɓen shugaban ƙasa

Ya zuwa ranar 6 ga Satumban 2023 idan Allah Ya kai mu, Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPT) za ta yanke hukunci game da ƙararrakin zaɓen shugabancin ƙasa da ke gabanta. Rajistaran Kotun Ɗaukaka Ƙara, Umar Bangari ne ya tabbatar da hakan a wani shiri da tashar Channels Television ta yi da shi ranar Litinin. Ya ce, “Kotun Ɗaukaka Ƙara na sanar da al'umma cewar za ta yanke hukunci a kan ƙararrrakin zaɓen Shugaban Ƙasa ya zuwa ranar Laraba, 6 ga Satumba 2023." Ƙararrakin sun haɗa ƙara mai lamba "CA/PEPC/03/2023 tsakanin Mr. Peter Gregory Obi & Anor da Hukumar…
Read More
Me ke kawo warin gaba

Me ke kawo warin gaba

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja, a yau za mu kawo maku wasu daga kayan gyara na mata, sai dai kafin nan zan so mu ɗan tattauna kan dalili ko dalilan da ke sa gaban mace wari. Gaban mace wuri ne da ke ɗauke da wani nau'i na ƙamshi da ya saɓa wa wanda gangar jiki ke fitarwa. Wannan ƙamshi dai a wurin wasu suna kiran sa da wari wanda ba a son jin sa, wannan dalilin ne ke sa wasu har turare suke sanyawa a gabansu don kawar da wannan…
Read More
Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (ƙarshe)

Dandalin shawara: Na kama matata da abokina, amma na kasa sakin ta (ƙarshe)

Tare Da AISHA ASAS TAMBAYA: Assalamu alaikum. Sunana……….daga……….. Na samu number daga hannun……..Dalilina na neman ki dai shi ne, abokina ne shi, na sanar da shi matsalar da nake tare da ita, sai ya ba ni number ki ya ce, na ma ki magana, wai kwanaki ma ke kin ka kashe matsalarsa da mai dakinsa. Wato mata nake da ita, kuma har ga Allah Ina masifar san ta, wannan ya sa nake kishinta ƙwarai da gaske. Ban rage ta da komai ba, duk abinda na mallaka zata iya iko da shi. Kuma ta ɓangaren kwanciyar aure daidai gwargwado ina duba…
Read More
Ya kamata mu san muhimmancin kanmu matasa

Ya kamata mu san muhimmancin kanmu matasa

Assalamu alaikum, kamar yadda na saba aiko da wasiƙu na duk mako a wannan jarida mai albarka, yau ma na zo da wata babbar wasiƙa na kira ga matasa, domin tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowace al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwa sakaka. Wajibi ne da ya hau kan al’umma ta yi tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su ƙaurace musu. Duk wata ƙasa…
Read More
Shin mun san kyautata wa iyaye na kawo cigaba a rayuwa?

Shin mun san kyautata wa iyaye na kawo cigaba a rayuwa?

Assalamu alaikum, na fahimci cewa kamar wasunmu ba mu san muhimmancin kyautata wa iyaye ba, duba ga irin zamanin da muke ciki yanzu, mun mayar da iyayenmu tamkar ba komai ba. Misali, a irin unguwar da nake, wasu matasan za ka ga kamar sun fi qarfin iyayen su, domin iyayen ba su isa su gaya musu komai ba su ji, wanda kuma nike ganin hakan bai kamata ba. Mu sani fa cewa, idan mutum ba ya kyautata wa iyayen sa, duk abin da ya ke nema a rayuwa ba zai tava samu ba, zai rinƙa shan wahalar banza ne kawai…
Read More
Sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar Gabon

Sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar Gabon

Sun soke zaɓen Shugaban Ƙasa Ali Bango na. Gabon wadda iyalan gidan suka shafe shekara 53 suna mulki lamarin da ya da suka kasance daga cikin shugabannin ƙasa da suka jima suna jan zaren su a karagar mulki a duniya. Soja sun yi juyin mulki tare da soke sakamakon zaɓe mai cike da maguɗi wanda aka jima ana zargin iyalan gidan Ali Bango da aikatawa, lamarin da ya sa ƙasar ke fuskantar ƙorafin siyasa da maguzin zaɓe. Libraville babban Birnin ƙasar Gabon na ƙunshe da ’yan ƙasar waje da ke gudanar da kasuwancin katako da sauran harkoki, kuma akwai ’yan…
Read More
Za mu ba da tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka wajen kama wasu masu laifi a Kano – ‘Yan Sanda

Za mu ba da tukwicin N1m ga duk wanda ya taimaka wajen kama wasu masu laifi a Kano – ‘Yan Sanda

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta ce tana neman wasu masu lafi biyu ruwa a jallo tare da cewa za ta bada tukwicin N500,000 kan kowannensu ga duk wanda ya taimaka da bayanai aka kama su. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Muhammed Sani Gumel ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wani babban mai laifi, Sadiq Ahmad wanda aka fi sani da Big Star, ɗaya daga cikin ɓatagarin da suka addabi al'ummar birnin Kano. CP Gumel ya ce da daɗewa sunan Sadiq Anmad na cikin jerin sunayen waɗanda rundunar ke nema ta kama, kuma ya shiga hannu ne sakamakon…
Read More
Tinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Tinubu zai yi wa shugabannin duniya jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 78 a hedkwatar majalisar da ke New York a ranar Talata 19 ga watan Satumba. Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa Tinubu, a ziyararsa ta farko zuwa Majalisar, zai yi jawabi ga shugabannin ƙasashen duniya da yammacin wannan rana. Shugaban na Nijeriya zai kasance shugaban Afrika na biyar da zai yi jawabi a rana ɗaya daga cikin taron, kamar yadda jerin sunayen masu gabatar da ƙara daga ofishin shugaban majalisar suka bayyana.…
Read More