Assalamu alaikum, kamar yadda na saba aiko da wasiƙu na duk mako a wannan jarida mai albarka, yau ma na zo da wata babbar wasiƙa na kira ga matasa, domin tabbas matasa na da muhimmancin gaske a kowace al’umma, tasirinsu ya fi gaban a zura ido kawai ga al’amura ko yanayin yadda suke gudanar da rayuwa sakaka. Wajibi ne da ya hau kan al’umma ta yi tattalin rayuwar matasa, samar da hanyoyin shigar da saqonnin abubuwa masu kyau don su siffantu da su, haka kuma a yi musu bayanin illolin abubuwa marasa kyau don su ƙaurace musu.
Duk wata ƙasa da ta ci gaba a wannan duniyar, idan aka waiwaiyi sirrin da ke tattare da samuwar ci gaban, za a ga a hannun matasansu yake. Saboda ba su yi sakaci a fannin kulawa da rayuwar matasan ba.
Haƙƙi ne babba wanda ya rataya a wuyan iyaye su kasance mataki na farko ta inda ’ya’yansu za su koyi tarbiyya, mu’amala da mutane da kiyaye dokokin ƙasa da kauce wa ayyukan varna da sauransu.
Idan iyaye suka gaza aikata hakan ga ’ya’yansu, babu tantama a daidai lokacin da yaron ya kai shekarun girma (matashi) ya fara mu’amala da waɗansu abokai a waje, za su koya masa dukan ɗabi’un da suka ga dama.
A wasu lokutan ma yanayin mu’amalar da ke tsakaninsa da su ne zai sa ya riƙa kwaikwayon yadda suke tafiyar da rayuwarsu a hankali har ya gina tasa ɗabi’ar.
Shekaru da dama muna ta addu’ar Allah Ya kawo mana shugabanni nagari a qasarmu, shekaru a baya iyayenmu suna ta cewa mu ne manyan gobe amma har yanzu ba mu da shugabanni masu tausayinmu, kuma har yanzu ba mu zama manyan goben ba.
To me ya jawo haka? Me ya sa har yanzu ƙasarmu ta qasa zama yadda muke fata kuma muke ta yi mata addu’a? Amsa ita ce mu matasa mun kasa fahimtar irin gudunmawar da za mu iya bayarwa domin qasarmu ta gyaru. Mun yi shiru mun kasa cewa uffan kan yadda ɓarayi ke ta kwashe dukiyoyinmu, mun yi shiru mun kuma kasa haɗuwa wuri guda domin mu haɗa kai mu gyara ƙasarmu.
Ba komai yake sa ni takaici ba illa yadda matasa muka yi sakaci da harkar ilimi! Ga mu da yawan gaske amma ba mu da aikin yi sai kallon ƙwallo da tafin ƙwallo da kuma yawon bangar siyasa.
Ga mu da yawan amma mun ƙi yarda mu nemi ilimi domin mu tallafa wa ƙasarmu.
Wassalam.
Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD.08168716583.