Shin mun san kyautata wa iyaye na kawo cigaba a rayuwa?

Assalamu alaikum, na fahimci cewa kamar wasunmu ba mu san muhimmancin kyautata wa iyaye ba, duba ga irin zamanin da muke ciki yanzu, mun mayar da iyayenmu tamkar ba komai ba.

Misali, a irin unguwar da nake, wasu matasan za ka ga kamar sun fi qarfin iyayen su, domin iyayen ba su isa su gaya musu komai ba su ji, wanda kuma nike ganin hakan bai kamata ba.

Mu sani fa cewa, idan mutum ba ya kyautata wa iyayen sa, duk abin da ya ke nema a rayuwa ba zai tava samu ba, zai rinƙa shan wahalar banza ne kawai a rayuwarsa. Kuma duk abin da ka yi wa iyayen ka, kai ma sai an yi maka ninkinsa, saboda haka mu kula.

Ya zama tilas a bautawa Allah, sannann a tautatawa iyaye, saboda kyautatawa iyaye zai kawo wa mutum ci gaba a rayuwarsa, kuma yana kyau mutum ya rinqa yi wa iyayen sa addu’a a koda yaushe tare da kyautata wa ’yan uwan sa da sadar da zumunci a tsakanin su.

Daga MUHAMMAD AUWAL MUSA (Ya Muha). 08062327373.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *