06
Sep
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kai ziyarar gani da ido a aikin hanyoyi da ake yi a Gusau, Babban Birnin Jihar. Aikin yana daga wani ɓangare na shirin bunƙasa birni da gwamnatin ta kawo, wanda kuma aka fara shi watan da ya gabata. Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnan ya bayyana farin ciki da yanayin da aikin ke tafiya. Ya ƙara da cewa, a yayin ziyarar duba aikin hanyar, dandazon jama’a ne suka yi wa gwamnan tarba ta musamman. Ya ce: “A ranar 18 ga watan Agustan…
