Editor

9513 Posts
Tinubu ya caccaki Obasanjo kan batun matatar man Fatakwal

Tinubu ya caccaki Obasanjo kan batun matatar man Fatakwal

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan kalaman da ya yi kan matatar mai da ke garin Fatakwal na Jihar Ribas. A wata hira da ya yi da manema labarai kwanan nan, Obasanjo ya jaddada cewa,  matatun man ƙasar ba za su taɓa yin aiki yadda ya kamata ba matuqar sun ci gaba da zama a ƙarƙashin gwamnati. “Wani ya gaya min cewa Tinubu ya ce matatun man za su yi aiki a watan Disamba. Na ce wa mutumin matatun man ba za su yi aiki ba. Wannan ya samo…
Read More
Yadda aka yi jana’izar Sheikh Giro Argungu a Kebbi

Yadda aka yi jana’izar Sheikh Giro Argungu a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi   An yi jana’izar shahararren malamin addinin Islama ɗin nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu, a mahaifarsa ta Argungu da ke Jihar Kebbi. Shehin malamin ya rasu ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC)  dake garin Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, bayan gajeriyar jinya. Kafin rasuwarsa shi ne Babban Sakataren Tsare-tsare na Ƙungiyar Izala ƙarƙashin jagoranacin Sheikh Bala Lau dake da sharkwata a Kaduna. Malam Giro ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa addinin Musulunci da ya yi sanadiyyar ɗaruruwan mutane karvar addinin Musulunci ciki da wajen Nijeriya. Malam Giro ya rasu ne yana da shekaru 61, inda…
Read More
Raɗɗa ya taya Tinubu murnar samun nasara a kotu

Raɗɗa ya taya Tinubu murnar samun nasara a kotu

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya taya Shugaban Ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu murna dangane da nasarar da ya samu a kotun sauraren ƙararrakin zaɓe, inda kotun ta tabbatar da nasarar zaɓen da aka yi wa Shugaba Tinubu tare da korar ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour Party suka shigar, inda suke ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar farkon shekarar nan. Raɗɗa ya bayyana cewar hukuncin kotun ya ƙara tabbatar da zaɓen da 'yan ƙasar nan suka yi wa…
Read More
Benjamin Kalu:  Gwagwarmaya da nagartar siyasa a majalisar tarayya

Benjamin Kalu:  Gwagwarmaya da nagartar siyasa a majalisar tarayya

Daga IMRAN ADAMU Masu iya magana dai kan ce, "Zakaran da Allah Ya nufe shi da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi". Zabbaben Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Benjamin Kalu yana kan kafa tarihi na zama fitacen dan siyasa da duka jam’iyyun siyasa ke alfahari da nasarar da ya samu.  Duba ga rayuwar Hon. Kalu a majalisa ta Tara (9th Assembly) ne farkon shigowarsa majalisa a matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisa da ke wakiltar mazaɓarsa ta Bende Federal Constituency daga Jihar Abia, amma hakan bai sa ya yi sanyin jiki a harkar majalisar da ta gabata ba wato…
Read More
Baki shi ke yanka wuya: Ƙwararan dalilai 22 da suka hana a naɗa El-Rufai minista

Baki shi ke yanka wuya: Ƙwararan dalilai 22 da suka hana a naɗa El-Rufai minista

Daga MUSBAHU BAFFA  Mutane da dama sun yi mamakin ganin yadda sunan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito cikin mutane ukun da Majalisar Dattawa ta ƙi tantance su. Sai dai yanzu wani binciken musamman da wata jarida ta yi ya tabbatar da cewa Hukumar SSS ce ta fitar da rahoto a kan sa dangane da waɗansu aika-aika masu nasaba da take haƙƙin ɗan Adam da kuma tulin kwafen ƙorafe-ƙorafen da aka riƙa aikawa a kan sa. Akwai zarge-zargen sa riƙa yin wasu kalamai ba tare da ya tunanin dai-dai ko rashin dacewar yin kalaman ba, ballantana kuma tunanin…
Read More
Duk macen aure na buƙatar tallafi ko mijinta na mata duk hidima – Jiddah Nguru

Duk macen aure na buƙatar tallafi ko mijinta na mata duk hidima – Jiddah Nguru

"Kasuwancin mata a kafafen sadarwa na ƙara masu ƙima a idon mabiyansu" Daga AISHA ASAS  A ci gaba da tattaunawa da matasan mata da ke da kishin kansu, waɗanda ke nema in ba kai ba ni wuri, shafin Gimbiya ya sake zaƙulo ɗaya daga cikin masu kasuwanci a kafafen sadarwa, don ta zama allon kallo ga mata irinta, kuma ta wayar da kai kan yadda mata za su iya cin moriyar intanet. Dama dai shafin naku ne mata, don haka muke kawo abinda zai ƙara maku ƙwarin gwiwa tare da ƙarfafaku kan dogaro da kanku. Masu hikimar magana dai sun…
Read More
Muhimmancin raya al’adun gargajiya ga rayuwar Hausawa

Muhimmancin raya al’adun gargajiya ga rayuwar Hausawa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A cikin wannan mako mai ƙarewa ne al'ummar Hausawa na faɗin duniya, musamman matasa, ɗalibai, marubuta, ’yan jarida da manazarta harshen Hausa suka suka gudanar da bukukuwan tunawa da al'adun gargajiya na Hausawa, a karo na uku cikin bainar jama'a, savanin yadda ake yi a baya ta kafafen sada zumunta a kowacce ranar 26 ga watan Agusta. Bincike ya nuna cewa, Ranar Hausa ta Duniya ko kuma International Hausa Day a Turance, rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen…
Read More
Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Allah Ya yi wa fitaccen malamin Islam na ƙungiyar JIBWIS, Sheikh Abubakar Giro Argungu, rasuwa. A ranar Laraba Allah Ya yi masa cikawa a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi bayan fama da rashin lafiya. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 68. Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya ba da sanarwar marigayin a shafinsa na Facebook a ranar Laraba. A na sa ran gabatar da jana'izar marigayin a wannan Alhamis kamar yadda Sheikh Bala Lau ya sanar.
Read More
Kotu ta kori ƙarar su Atiku kan Tinubu

Kotu ta kori ƙarar su Atiku kan Tinubu

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe mai zamanta a Abuja ta kori ƙarar da Jam'iyyar PDP da ɗan takararta na shugabancin ƙasa, Atiku Abubakar suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata. Kotu ta yi watsi da ƙarar ne a zaman shari'a da ta yi ranar Laraba. Yayin zamanta, kotun ta soke wasu sakin layi a ƙorafin da aka shigar da suke nuni da Shugaba Bola Tinubu bai cancanci shiga zaɓen da ya gudana ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata ba. Ta ce masu ƙarar sun gagara gabatar wa kotun cancantar…
Read More
Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa: Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotu

Shari’ar zaɓen shugaban ƙasa: Jam’iyyar Labour ta yi watsi da hukuncin kotu

Jam'iyyar Labour Party ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa kan ƙarar da ta shigar tana ƙalubalantar nasarar da Shugaba Tinubu ya samu a babban zaɓen da ya gabata a watan Fabrairu, 2023. Cikin sanarwar da ta fitar bayan hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Obiora Ifoh, ya ce ba a yi wa LP adalci ba kan ƙarar da ta shigar kan jam'iyyar APC da Tinubu. Ya ce jam'iyyar tasu za ta ɗauki mataki na gaba bayan tuntuɓar lauyoyinta bayan kuma ta amshi takardar shaidar hukuncin da kotun ta…
Read More