08
Sep
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami'ar nan mai zaman kanta mai suna Azman University da ke Kano, za ta fara yin digiri a fannin koyon tuƙin jirgin sama wanda ya ke shi ne na farko a Nijeriya da ma Afirka ta Yamma. A zantawarta da manema labarai da ya gudana a harabar makarantar da ke 'Yargaya da ke kan titin Wudil ranar Talata, Shugabar Jami'ar Farfesa Fatima Batulu Muktar ta bayyana cewa Jami'ar Azman ta samu sahalewar yin kwasa-kwasan tuqin jirgin sama guda biyu da suka haɗa da; Aviation Management da kuma Aviation Security. Ta kuma ce Jami'ar Azman za…
