11
Sep
Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a Jihar Kano ta tsige Yusuf Umar Datti na Jam'iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kura/Madobi/Garun Malam a jihar. Bayan tsige Datti daga kujerar ɗan majalisa tmda ta yi, kotun ta ayya abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Musa Ilyasu Kwankwaso, a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta kama Datti da laifin ƙin ajiye aikin gwamnati a tsakanin kwana 30 kafin shiga zaɓe kamara yadda doka ta tanada. Kafin shiga zaɓen, ɗan siyasar ma'aikaci ne a Jami'ar Bayero ta Kano. Kazalika, Alƙali Azingbe ya ce…
