Dangantaka na ƙara tsami tsakanin Gwamna Obaseki da mataimakin sa

  • Ana yunƙurin fitar da ofishin mataimakin daga fadar gwamnati Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rikicin da ke tsakanin Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki da mataimakinsa, Philip Shaibu na ci gaba da ruruwa yayin da ake shirin mayar da mataimakinsa wani gini da ke wajen gidan gwamnati.

Ginin da ke lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, kusa da gidan gwamnati, wanda shine ofishin hukumar saye da sayarwa ta jihar Edo, an gyara shi domin ya zama ofishin mataimakin.

Tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole ne ya qaddamar da ginin a ranar 16 ga watan Disamba, 2014.

Sai dai kuma da aka tuntuɓi babban sakataren yaɗa labarai na Shaibu Musa Ebhomiana, ya ce batun komawa kowane ofishi jita-jita ne domin ba a sanar da mataimakin gwamnan kan hakan ba.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka gani a wurin, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce ana sa ran za a gudanar da aikin a ranar Litinin.

A cewarsa, “Ina aiki da kamfanin da ke kula da gyaran wannan ginin. Aikinmu shi ne gabatar da aikin a ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa “Ban ni da masaniyar amfanin da za a yi da ginin.”

Kwamishinan Sadarwa da Yaɗa Labarai, Chris Nehikhare ya ce: “Idan akwai alamar gwamnati da ke cewa haka, to lallai ya zama haka.”

Ku tuna cewa dangantaka tsakanin fitattun jagororin biyu ta yi tsamani ne a lokacin da Shaibu ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja domin ta dakatar da tsige shi.

Sai dai gwamnan da kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, sun musanta hakan.

Watakila Shaibu ya fusata gwamnan ne saboda burinsa na ya gaji ubangidansa, wanda ya dage cewa lokaci ne na Edo ta Tsakiya da ya kawo gwamnan jihar.

A wani taron mabiya addinai da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Lahadin da ta gabata, jami’an tsaro sun hana mataimakin gwamnan samun damar ganawa da gwamnan, a ranar da ya yi mubaya’a ga Obaseki, amma ya ce burinsa na zama gwamna (Shaibu) na nan daram.

Wasan ya rikiɗe zuwa mummuna a ranar Litinin da ta gabata inda gwamnatin jihar ta rusa tawagar mataimakin gwamnan jihar ta kafafen yaɗa labarai bayan wani hatsaniya da aka yi da safiyar ranar a wani taron jihar da ya kai Shaibu ya fice daga wurin taron.