Minista Malagi a mizani

Ga duk wanda ya fahimci Malagi a natse kuma ya iya fahimtar yadda haƙuri da jajircewa ke zamowa sular ɗaukakar mutum za a iya tabbatar da cewa lallai mun dace da miqa wa Alhaji Muhammed Idris Malagi muƙami na minista a fannin labarai.

Kakakin na Nufe na da kyakkyawan hali na haƙuri wanda tun a neman takara ta gwamna a jihar su Neja wanda abokin takarar sa Alh Bago ya samu.

Malaji bai koma gefe ya riƙa surutai da soke soke ba wanda hakan wata al’ada ce wacce da dama yan siyasar mu ta zamo ma su jiki duk wanda ya nema ya samu a nan ne a kai adalci amma idan an gaza cimma nasara a nan ne an yi rashin adalci imma daga kotu a sauya jam’iyya ko kuma a zauna a cikin ta domin kulla ma ta maƙarƙashiya ta zamon ƙasa.

Malagi bai yi haka ba duk da ina a jihar mu katsina da ya yi kwatankwacin haka da mun ji.

Tabbas nufawa ku na da naku abun na yabawa duk kuwa da ba a rasa kurakurai a rayuwa ba. Da fatan wannan muƙami ya ƙara fito da kimarka.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *