12
Sep
Fitaccen ɗan jarida a fannin ɗaukar hoto a Nijeriya, Sani Maikatanga, ya lashe gasar ɗaukar hoto ta ƙasa da ƙasa ta Wiki Loves Africa 2023. Mutum 13,413 daga ƙasashen Afirka 51 ne suka shiga gasar. Maikatanga ya yi wa takwarorinsa zarra a gasar ne ta dalilin wani hoto da ya ɗauka mai alaƙa da sauyin yanayi a ƙauyen Auyo, Jihar Jigawa. Taken gasar na bana ya maida hankali ne kan sauyin yanayi. Bayanan Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, (WHO), sun nuna sauyin yanayi matsala ce da kan shafi iskar da ake amfani da ita da ruwan sha da abinci da…
