Editor

9513 Posts
Gwamnatin Kebbi ta bai wa ɗan gidan Giro muƙami a hukumar Alhazai

Gwamnatin Kebbi ta bai wa ɗan gidan Giro muƙami a hukumar Alhazai

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Gwamna Malam Nasir Idris ya maye kujerar Marigayi Sheikh Abubakar Abddullahi Giro Argungu da ɗansa Malam Hussaini Abubakar Giro a hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Kebbi, inda Sheikh Abubakar Giro kafin rasuwarsa mamba ne a hukumar. Wannan ya biyo bayan wani koke da ƙungiyar Izala ta ƙasa ƙarƙashin jagoranacin Sheikh Bala Lau ta miƙa wa Gwamna Idris ne yayin da suka je ta'aziyya a fadar gwamnatin jihar Kebbi inda suka nemi gwamnati da ta janyo ɗaya daga cikin 'ya'yan Marigayi Giro a jiki saboda cigaba daga inda ya tsaya. Gwamna Malam Nasir Idris ya…
Read More
Wasannin da ke gaban Real Madrid cikin watan Satumba

Wasannin da ke gaban Real Madrid cikin watan Satumba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Real Madrid za ta buga wasa biyar a cikin watan Satumba nan gaba, ciki har da huɗu a gasar La Liga da daya a gasar Zakarun Turai. Kenan cikin mako biyu za ta yi karawa biyar, wadda za ta fara da karvar baƙuncin Real Sociedad ranar Lahadi 17 ga wata a wasan mako na biyar a La Liga. Real Madrid, wadda ta ke ta ɗaya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya na fatan lashe karawar domin ta ci gaba da jan ragama. Kwana uku tsakani da fuskantar Sociedad za ta buga wasan farko a…
Read More
Zargin cin hanci: Gwamnatin Kano ta dakatar da manajan kamfanin KASKO

Zargin cin hanci: Gwamnatin Kano ta dakatar da manajan kamfanin KASKO

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A wani yunƙuri da gwamnatin jihar ke yi na yaƙi da cin hanci da rashawa, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin dakatar da Manajan daraktan kamfanin samar da aikin gona na Kano (KASCO), Dakta Tukur Dayyabu Minjibir. Ta cikin wata sanarwar da Babban Sakataren yaɗa yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, ta ce Gwamnan ya bayar da umarnin dakatarwar ne a Laraba, wanda Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya miƙa. An dai dakatar da Manajan Darakta ne bisa zargin hannu a sayar da hatsin…
Read More
Har yanzu akwai tsofaffin marubutan da ba su yarda da rubutun onlayin ba – Jamila R/Lemo

Har yanzu akwai tsofaffin marubutan da ba su yarda da rubutun onlayin ba – Jamila R/Lemo

"Na samu kaina a harkar rubutu tun Ina 'yar shekara tara" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk mutumin da ya kasance tsohon makarancin littattafan Hausa ne, musamman littattafan da jajirtattun mata gwanayen riqe alqalami suka wallafa a shekarun baya, ba zai kasa karanta littafin Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ba, marubuciyar 'Mamaya', 'Zaƙi Da Maɗaci', da Bakin Ganga. Wacce bayan kasancewarta marubuciya har wa yau kuma ma'aikaciya ce ƴar jarida, da ta daɗe tana bayar da gudunmawa a harkar ilimi da cigaban al'umma. Littafinta na 'Kanya Ta Nuna' da ta fara bugawa a shekarar 2002 ya kasance zakaran gwajin dafi, wanda…
Read More
Babu amfanin samun mace in har ba za ta taimaki mijinta ba – Jiddah Haulat Nguru (2)

Babu amfanin samun mace in har ba za ta taimaki mijinta ba – Jiddah Haulat Nguru (2)

"A wannan zamani sana'a kamar dole ta zamewa 'ya mace" Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mai karatu idan bai manta ba, mun ɗauko fira da matashiya Jiddah Haulat Nguru, inda ta fara bayyana mana tarihi da kuma irin sana'ar da take yi, wadda ta tabbatar mana ana cin kasuwarta ne a kafafen sadarwa, sannan ta yi mana bayanin yadda ta fara, da hanyoyin da take bi don siya da siyar da kayanta a kafafe kamar Fesbuk, WhatsApp da sauransu. A wannan satin, za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. Kamar yadda muka sanar, baƙuwar tamu za…
Read More
Cin amanar makusanta ga cin zarafin ƙananan yara

Cin amanar makusanta ga cin zarafin ƙananan yara

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na samu halartar wani taron ƙaddamar da littafin da wata matashiyar marubuciya ta wallafa da harshen Turanci, mai suna Shackles of Abuse, wato Sarƙaƙiyar Cin Zarafi, labarin bautar da ’ya’ya mata cikin lalata. Ko da yake ba ina son yin sharhi kan littafin ba ne, sai dai labarin da jigon littafin ya taɓo ne ya tava zuciyata, kuma na ga ya dace mu yi nazari a kansa cikin wannan mako. Labaran da ke cikin wannan littafin suna da tsoratarwa da firgitarwa ainun, musamman irin yadda marubuciyar ta riƙa kwatanta halin da ta samu kanta a…
Read More
Tarihin yaƙin duniya na farko

Tarihin yaƙin duniya na farko

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A tarihi, yaƙin duniya na ɗaya wanda a Turance ake kira da ‘World War I’ ko ‘First World War’ wani yaqi ne wanda manyan ƙasashen duniya, musamman na nahiyar Turai (Europe) irin su Ingila (Britain), France, Germany, Russia, Austria-Hungary, Russia, Daular Ottoman ta Turkiya (Ottoman Empire), da kuma Amurka suka fafata, a tsakanin shekarun 1914 zuwa 1919. A bisa tarihi, ya tabbata cewa zuwa shekarar 1900 wato farkon ƙarni na 21, ƙasashen yammacin Turai irin su Ingila, France, Germany, Spain, Portugal, Netherlands, da kuma Italy sun kai ga cikakken ci gaban tattalin arziki (economic development) da…
Read More
Rahoton aukuwar zanga-zanga a fadata saboda kisan manoma ba gaskiya ba ne, cewar Sarkin Gwoza

Rahoton aukuwar zanga-zanga a fadata saboda kisan manoma ba gaskiya ba ne, cewar Sarkin Gwoza

Sarkin Gwoza a Jihar Borno, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya ƙaryata rahoton da aka yaɗa a soshiyal midiya kan cewa wasu fusatattun mazauna yankin sun yi zanga-zanga a fadarsa saboda kashe wasu manoma da 'yan Boko Haram suka yi a yankin. Basaraken ya ƙaryata rahoton ne a tattaunawar da ya yi da jaridar Vanguard a ranar Talata. A cewarsa, "Jita-jitar da ake yaɗawa a soshiya midiya cewa fusatattu a Gwoza sun mamaye fadata kan kisan manoma da garkuwa da wasu a baya-bayan nan, hakan ba gaskiya ba ne." Sarkin ya tabbatar cewa lalle ne 'yan bindiga sun kashe manoma biyar…
Read More
Raba-gardama: Waƙoƙin zamani rubutattu ne ko na baka?

Raba-gardama: Waƙoƙin zamani rubutattu ne ko na baka?

Daga MUHAMMAD ILIYASU (MD Asnanic) 1.0 GABATARWA Masana, musamman na ɓangaren limin addinin Musulunci, sun bai wa sanin abu (ilimi) wasu darajoji hawa-hawa har zuwa hawa uku: daraja ta farko ita ce 'haƙƙul-yaƙini' (ilimin da ke tare da mutum yake jin sa a cikin jikinsa, kamar wata cuta da ke cin sa a cikin jikinsa), daraja ta biyu kuma 'aynul-yaƙini' (ilimin da ka gan shi muraratan, misali idan aka ce maka cuta kaza tana illa kaza kuma sai ka ga illar a jikin na tare da kai), daraja ta uku kuwa ita ce 'ilimul-yaƙini' (shi ne ilimin da za a…
Read More
Zuwa ga ‘yan mata: Binciken aure ba aikin iyaye ne kaɗai ba

Zuwa ga ‘yan mata: Binciken aure ba aikin iyaye ne kaɗai ba

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku na zamantakewa na jaridarku mai fari jini ta Manhaja. A wannan mako za mu tattauna a kan yadda budurwa ko bazawara za ta taya iyayenta bincike a kan mijin da suka daidaita, kuma suke fatan su raya sunnar Annabi SAW ta auren juna da za su yi. Menene bincike a aure? Kamar yadda muka sani a ƙasar Hausa, da wuya a ce an yi aure ba tare da iyayen yarinya sun yi bincike a kan wanda ya zo neman auren ɗiyarsu ba. Wato za su…
Read More