Zuwa ga ‘yan mata: Binciken aure ba aikin iyaye ne kaɗai ba

Tare Da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku na zamantakewa na jaridarku mai fari jini ta Manhaja. A wannan mako za mu tattauna a kan yadda budurwa ko bazawara za ta taya iyayenta bincike a kan mijin da suka daidaita, kuma suke fatan su raya sunnar Annabi SAW ta auren juna da za su yi.

Menene bincike a aure?

Kamar yadda muka sani a ƙasar Hausa, da wuya a ce an yi aure ba tare da iyayen yarinya sun yi bincike a kan wanda ya zo neman auren ɗiyarsu ba. Wato za su bincika su ga su waye iyayensa, kuma wacce sana’a yake, meye ɗabi’unsa a unguwa da makamantansu.

Shin kwalliya tana biyan kuɗin sabulu idan an yi binciken?

To, ba za a ce kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu ba tunda wasu abubuwan ana iya ganowa. Amma gaskiyar magana wannan binciken akwai ya babu sunasa. Domin wasu lokutan ana samu matsala da binciken. Akan samu rufa-rufa a wajen mutanen da ake tambaya saboda suna tsoron a ce sun ɓata aure.

Ko kuma suna tsoron su faɗi gaskiya, amma suna tsoro kar a ce suna baƙin ciki da auren ko kuma sun san ma ko sun faɗa ba zai amfani ba domin faɗar ba ta hana auren ya tabbata. Sannan kuma, wani zubin binciken kan tashi a banza. Domin duk iya binciken wani zubin wata halayyar ma’auratan sai zama ya yi zama sannan ake fuskanta. Ka ga ba lallai wasu abubuwan dole a gano su yayin bincike ba.

Ina mafita?

Mafita ita ce, su ‘yammatan da zawarawan da aka zo aura su ya kamata su dinga taya iyayensu wani binciken. ‘Yaruwa, ba wanda zai zauna miki da mijin nan sai ke, kuma iyayenki da danginki ba su za su zauna da shi ba. Kuma ba su suke mu’amala da shi ba, ke ce. Ki buɗe idanunki da kyau, aure abu ne na dindindin ba wucin gadi ba ne. Mance da ƙaguwarki da son auren da kike yi.

Kuma ki mance da yadda yake tarairayarki kamar ƙwai. Sai an zo zaman aure ake yin gaskiya da gaskiya. Idan ba ki buɗe ido kin rarrabe da baccin makaho ba za ki sa rayuwarki a cikin ƙunci marar yankewa. Meye amfanin doguwar waya da hira ta Wasaf ko Fesbuk da kuke yi, idan ba za ki nutsu ki gano wasu ɗabi’u nasa ba da ba za ki iya jure rayuwa da su ba? Iyayenki sun gama nasu aikin na gano miki shi ɗin mutumin kirki ne. Kuma sun gano yana da halin riƙe ki ko a’a.

Amma ke ke ce za ki yi wa kanki alƙalanci ki gane ko halayya da fahimtar junanku ta dace da juna ko ‘yan kun ji-kun ji da ba za a rasa ba. Domin mutanen kirki guda biyu za su iya samun matsala a aure. Domin ba kowacce matsala ce da ake samu a aure ba sakamakon rashin kirkin ma’auratan ba. Wasu abubuwan na iya jawo matsalolin da ba ku shirya ba.

Ga wasu abubuwan da ya kamata mace ta tantance kan mjin da za ta aura, tun kafin ma ta bari alaƙar ta yi nisa har a kai ga turo iyaye. In dai kin yi amfani da hankali da nutsuwa za ki ya gano su. A yadda yake faɗar abubuwa da yadda yake ba ki labarun mutanensa da yadda…

Waye shi, sana’arsa, tarihin rayuwarsa, burinsa, halayyarsa, abinda yake so da wanda ba ya so.

Kin tabbatar kina sonsa har ranki? Son da kike masa zai kai ki iya haƙuri da duk wani naƙasunsa kuma ki yafe masa idan ya saɓa miki bayan kun yi aure? Domin bahaushe fa ya ce, zo mu zauna, zo mu saɓa.

A yadda kike gani, akwai alamun iyayensa sun karɓi batunki hannu bi-biyu?

Idan mai fushi ne, za ki iya jure fushinsa bayan kun yi aure? Domin yanayin fushin da yake nuna miki a yanzu bai wuce wani ƙaramin kaso na ainahin fushin da yake da shi ba. Kin shirya jurewa bayan kun yi aure?

Yana da ra’ayin kansa ko ɗan a bi yarima a sha kiɗa ne, sai abinda abokai ko ‘yanuwansa ko matarsa suka ce masa?

Kuna samun raha da juna ba tare da cikas ba? Idan kika ba shi shawara yana amsa, kuma yana gyara kura-kurensa?

Yana da halin ɗaukar ɗawainiyar dukkan buƙatunki? Yana miki ƙarya? Ɓangaren addininsa fa? Yana da tsoron Allah?

Kin san rkunin jininsa da tsarin ƙwayar halittarsa ta Genotype? Naki iyayen sun karɓe shi ba matsala? Yana da alƙibla?

Alƙiblarsa ta dace da taki? Yana da halayya da mu’amalar da za ki so samu tattare da mijin da za ki aura? Akwai alamar yana shan taba ko kayan maye?
Marowaci ne? Yana yi miki wulaƙanci da gadara?

Ki tabbatar da kin samu waɗannan amsoshin kafin ki kai ga amince masa ya turo gidanku maganar aure. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira. Sai wani makon kuma idan rai ya kai.