Editor

9513 Posts
Dimokuraɗiyya ba ta da riba muddin ba ta kawo cigaban al’umma – Malagi

Dimokuraɗiyya ba ta da riba muddin ba ta kawo cigaban al’umma – Malagi

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Alhaji Muhammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, dimokuraɗiyya ba ta da wani amfani muddin ba za ta haifar da cigaba da haɗin kan al'umma ba. Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai a Ma'aikatar, Suleiman Haruna, ya ce Ministan ya bayyana haka ne yayin da mambobin jam'iyyar APC na shiyar Arewa ta Tsakiya suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja a ranar Juma'a. “Wannan ne ma ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa batun haɗin kai da bunƙasa tattalin arziki muhimmanci ga jama'armu, ni ma wannan shi ne saƙon da nake…
Read More
Guardiola zai ja ragamar wasan Man City da West Ham bayan dawowa daga jinya

Guardiola zai ja ragamar wasan Man City da West Ham bayan dawowa daga jinya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ana sa ran Pep Guardiola zai koma Ingila ranar Laraba, domin jan ragamar wasan da Manchester City za ta kara da West Ham a gasar Firimiyar Ingila. Ranar Asabar 16 ga watan Satumba City za ta ziyarci West Ham, domin fafatawa a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila. City tana matakin farko a kan teburi da maki 12, bayan cin dukkan wasa huɗu da fara kakar nan, yayin da West Ham mai maki 10 take ta huɗu. Guardiola, wanda ya yi jinya sakamakon ciwon baya, bai ja ragamar City wasan Firimiya da…
Read More
Gwamnan Kano ya kori Kwamishina kan kalaman tunzura al’umma

Gwamnan Kano ya kori Kwamishina kan kalaman tunzura al’umma

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallami Kwamishinan Filaye da Safiyo na gwamnatin jihar, Adamu Aliyu Kibiya, daga muƙaminsa bayan zargin sa da furta kalaman tunzura al’umma. Kazalika, sallamar ta shafi mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin wasanni da matasa, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye wanda shi ma ake zargi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatin. Idan za a iya tunawa, a ƙarshen makon nan ne bidiyon jami’an gwamnatin suka rinƙa yawo a shafukan sada zumunta, inda suke furta kalamai game da shari’ar da ake…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya naɗa Yemi Cardoso Gwamnan CBN

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya naɗa Yemi Cardoso Gwamnan CBN

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da a naɗa Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), na wa'adin shekara biyar ya zuwa lokacin Majalisar Dattawa za ta tabbatar da naɗin nasa. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, a ranar Juma'a. Sanarwar ta ce naɗin ya yi daidai da Sashe na 8 (1) na Dokar Babban Bankin Nijeriya na 2007, wanda ya sahale wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa Gwamnan CBN da mataimaka huɗu gabanin Majalisar Tarayya ta tabbatar da naɗinsu. Kazalika, Bola…
Read More
Ma’aikatan lafiya 400,000 sun yi kaɗan a Nijeriya, inji minista

Ma’aikatan lafiya 400,000 sun yi kaɗan a Nijeriya, inji minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Lafiya da Walwalar Al'umma, Ali Pate, ya ce ma'aikatan kiwon lafiya 400,000 a Nijeriya ba su isa ba wajen biyan buƙatun kiwon lafiyar 'yan Nijeriya. Pate ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, bayan ganawar kwanaki uku da ya yi da sassa da hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar. Ma'aikatar ta shirya taron ne domin fitar da wani tsari na tsarin kiwon lafiya a Nijeriya. A cewar Pate, ma’aikatan fannin lafiya dubu 400,000 sun haɗa da ma’aikatan kiwon lafiya na al’umma, ma’aikatan jinya, ungozoma,…
Read More
An dakatar da Pogba kan zargin yi wa kansa allurar ƙara kuzari

An dakatar da Pogba kan zargin yi wa kansa allurar ƙara kuzari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An dakatar da ɗan wasan Juventus, Paul Pogba kan zargin karya dokar shan abubuwan kara kuzari ga 'yan wasa. Hukumar Hana Shan Abubuwan Ƙara Kuzarin Wasa ta Italiya (NADO) ta ce, ta samu wani sinadari fiye da ƙima a jikin Pogba, bayan tashi daga karawar da Juve ta ci Udinese 3-0 ranar 20 ga watan Agusta. Ɗan ƙwallon na tawagar Faransa, mai shekara 30 ya yi zaman benci a karawar, amma aka zaɓo shi cikin jerin 'yan wasan da aka gwada bayan karawar. Idan aka samu Pogba da laifi za a iya dakatar da shi shekara…
Read More
Za mu magance matsalar cin zarafin mata a hidimar ƙasa – Daraktan NYSC

Za mu magance matsalar cin zarafin mata a hidimar ƙasa – Daraktan NYSC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Darakta Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) Brig Gen. Yushau Ahmed, ya ce za su magance matsalar cin zarafin mata a NYSC. Babban daraktan wanda ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin gangamin wayar da kan al’ummar karkara a Bauchi, ya ce shirin ya dade yana yaqi da GBV ta hannun ƙungiyar ta Corps Gender Vanguards. Darakta Janar na hukumar ta NYSC a Jihar Bauchi, Misis Rifkatu Yakubu, ta wakilce shi, ta bayyana cewa, an samar wa Vanguards kayayyakin aikin da suka dace don gudanar da gangamin wayar da kan…
Read More
Gwamnatin Borno za ta rufe makarantu 300 masu zaman kansu

Gwamnatin Borno za ta rufe makarantu 300 masu zaman kansu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fiye da makarantu masu zaman kansu 300 a Borno su na fuskantar barazanar rufewa saboda gaza shiga cikin takardar izinin gwamnati. Kwamishinan Ilimi Injiniya Lawan Wakilbe, ya shaida wa manema labarai a Maiduguri a ranar Laraba cewa, matakin ya zama dole domin daƙile yaduwar ayyukan wasu makarantu masu zaman kansu. Ya ce akwai damuwa cewa tun da aka fara atisayen a shekarar 2022 makarantu masu zaman kansu 266 ne kawai suka cika sharuɗɗan, daga cikin kusan 600. Wakilbe ya ce ma’aikatar, masu makarantu masu zaman kansu, ma’aikatar shari’a da ’yan sanda za su yi taro a…
Read More
PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da almubazzarancin Biliyan N20 cikin kwana 100

PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da almubazzarancin Biliyan N20 cikin kwana 100

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Jam'iyyar PDP ta adawa a Jihar Kebbi ta zargi gwamnatin jihar ta Kebbi da almubazzaranci da zunzurutun kuɗi har Naira billiyan ashirin a cikin kwanaki 100 kacal. Alhaji Usman Bello Suru shugaban jam'iyyar PDP ne ya bayyana haka a wata zantawa da manema labarai a garin Birnin Kebbi, yayin da gwamnatin ke gudanar da bikin cika kwanaki 100 da gwamnatin APC ta yi a kan mulki. Ya ce ta yaya gwamanti za ta kashe har Naira billiyan 20 wajen gyaran babban birnin jihar kaɗai ba tare da la'akari da irin yadda yanayin al'umma ya ke…
Read More