17
Sep
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon sojin ruwan Nijeriya, Rear Admiral Yaminu Musa (mai ritaya), Shugaban Gudanarwa na Cibiyar Yaqi da Ta’addanci a ofishin mai baiwa shugaban qasa shawara kan harkokin tsaro (NCTC-ONSA) ya ce ana amfani da kuxaxen da ake samu na garkuwa da mutane ne wajen samar da kuxaxen ta’addanci. Musa ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja yayin taron ‘Anti-Kidnap Multi-Agency Fusion Cell Media and Communication Workhop’ wanda ONSA tare da haxin gwiwar babbar hukumar Birtaniya ta shirya. “An kuma bayyana satar mutane don neman kuxin fansa a matsayin xaya daga cikin hanyoyin samar da kuxaxen…
