Editor

9513 Posts
‘Yan ƙasa ga Tinubu: Ba ma buqatar tallafin rage raɗaɗi, a rage mana farashin fetur kawai

‘Yan ƙasa ga Tinubu: Ba ma buqatar tallafin rage raɗaɗi, a rage mana farashin fetur kawai

*A zuba kuɗin tallafin rage raɗaɗi zuwa harkar ilimi da lafiya - 'yan ƙasa*Tallafin rage raɗaɗi ba shi da wata ma'ana - Inji ɗan kasuwa*Dole gwamnati ta sake tunani – Kwamared Alifia Daga AMINA YUSUF ALI A ƙoƙarinta na rage raɗaɗi da wahala da 'yan ƙasa suke sha a sakamakon cire tallafi a kan man fetur, gwamnatin tarayya ta shigo da tsarin ba da tallafin rage raɗaɗi, amma 'yan Nijeriya da suka samu kansu cikin matsuwa irin ta tattalin arziki sun fito sun bayyana cewa, sun fi qaunar a rage farashin man fetur fiye da tallafin rage raɗaɗin. Shugaba Bola…
Read More
Shari’ar Gwamnan Kano: Kotu ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci

Shari’ar Gwamnan Kano: Kotu ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Kano ta ayyana ranar Laraba ta wannan mako a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke gabanta inda Jam'iyyar APC ke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata. A ranar Litinin da ta gabata Kotun ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin cikin sanarwar da ta aike wa ɓangarorin da shari'ar ta shafa. Sakataren lauyoyin NNPP, Barrister Bashir T/Wurzici, ya tabbatar wa Jaidar Daily Trust da hakan, yana mai cewa lallai an miƙa wa tawagar lauyoyi takardar…
Read More
Tinubu ya naɗa Nkwocha, Kakanda da wasu a muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu ya naɗa Nkwocha, Kakanda da wasu a muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon Editan Jaridar Leadership, Kingsley Stanley Nkwocha, a matsayin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai a Fadar Shugaban Ƙasa. An naɗa Nkwocha tare da wasu ne inda za su yi aiki tare a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. Kazalika, Tinubu ya naɗs Tope Fasua a matsayin Mai Bada Shawara na Musamman Kan Harkokin Tattalin Arzikin Ƙasa a ofishin Mataimakin na Shugaban Ƙasa. Sauran waɗanda aka naɗa masu bada shawara a ɓangarori daban-daban sun haɗa da Sadiq S Jambo da Dr. Muhammad Bulama da Mahmud Muhammad da kuma Ahmed Ningi. Sanarwar…
Read More
Tinubu ya naɗa Baba-Ahmed mai bai wa mataimakinsa shawara

Tinubu ya naɗa Baba-Ahmed mai bai wa mataimakinsa shawara

Hakeem Baba-Ahmed, a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban, Kashim Shettima. Baba-Ahmed da kansa ya sanar da naɗin nasa a shafinsa X a ranar Litinin. “Lokaci ne da ya kamata in bayyana wa duniya cewa na amsa kira in yi aiki a matsayin Mai Bada Shawara ns Musamman (kan harkokin siyasa) ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettim,” in ji shi Shi ɗin jigo ne a Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), kuma ɗan uwa ga abokin takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar Labour a babban zaɓen da ya gabata, wato Datti Baba-Ahmed. Ya…
Read More
Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamnan Zamfara

Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamnan Zamfara

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Jihar Zamfara, ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya samu a babban zaɓen da ya gabata. Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin. Bala Idris ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin tabbatar da zaɓin al'ummar jihar ta Zamfara. Dauda Lawal ya zama gwamnan Zamfara ne biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a watan Maris da ya gabata, inda ya ɗaɗa gwamana mai ci na wancan lokaci da ƙasa. “Ba da jimawa…
Read More
Ashe jami’an lafiya 400,000 ne a Nijeriya

Ashe jami’an lafiya 400,000 ne a Nijeriya

Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Lafiya uwar jiki inji masu iya magana inda har su ka ƙarasa da cewa babu mai fushi da ke. A gaskiya yawancin mu ba za mu fahimci muhimmancin kiwon lafiya ba sai in mun samu ƙalubalen rashin lafiya. Ba ma nan matsalar ta ke ba sai lokacin da mutum ya samu matsalar rashin lafiya ya ruga asibiti zai gane ashe ba sauƙi lamarin ya ke da shi ba. Wato mutum ya samu likita ya duba shi don a rubuta ma sa magani da zai shiga shagon sayen magani ya saya da kuɗin sa ma aiki…
Read More
Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Illolin shaye-shayen ƙwayoyi da hanyoyin shawo kan lamarin

Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al'umma musamman ma matasa maza, wanda babban abin takaici halayya ce da aka fi dangantawa ga maza, sai ga shi ta zama ruwan dare har mata sun fi maza iyawa. Masu aure da waɗanda ba su da shi, shaye-shaye na nufin duk wani yanayin da ɗan adam zai saka kan shi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarin shi ta yadda ba zai iya bambanta ya kamata da akasin hakan ba. A zamanin baya, muna jin labarin irin waɗannan ɗabi’un a ƙasashen ƙetare, wasa-wasa har ta shigo cikin ƙasarmu da al’ummarmu. Da yawa mutane…
Read More
Gwamnati ta ƙaryata yunƙurin juyin mulki a Congo

Gwamnati ta ƙaryata yunƙurin juyin mulki a Congo

Gwamnatin Ƙasar Congo Brazzaville ƙarƙashin jagorancin Shugaba Denis Sassou Nguesso ta ƙaryata yunƙurin juyin mulki a ƙasar. Ta bayyana haka ne cikin wani saƙo da ta wallafa a Tiwita a ranar Lahadi. Kafafen yaɗa labarai da dama sun ruwaito ranar Lahadi cewar sojoji ana yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar a yayin da Shugaban Ƙasar yi tafiya. Saƙon X (Tiwita) da Ministan Sadarwa da Yaɗa Labarai na Ƙasar, Thierry Moungalla, ya wallafa a shafinsa ya ƙaryata haka. “Gwamanati ta ƙaryata rahoton. Muna sake jaddada wa al'umma zaman lumanar da ke akwai a ƙasar, muna kira ga jama'a kowa ya ci gaba…
Read More
Tinubu ya naɗa ministocin matasa

Tinubu ya naɗa ministocin matasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da a naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim Ministar Matasa gabanin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin. A cewar mai magana da yawun Shugaban Ƙasa a ranar Lahadi, Ajuri Ngelale, Tninubu ya kuma amince da naɗin Mista Ayodele Olawande a matsayin Ƙaramin Ministan Matasa kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasa nan gaba. “Dr. Jamila likita ce wadda ta yi shugabancin Ƙungiyar Cigaban Mata Matasa (PYWF) ba da daɗewa ba. "Kazalika, ta riƙe muƙamin Hadimar Gwamnan Jihar Kwara kan Muradan Samar da Cigaba Mai Ɗorewa (SDGs). “Shi kuwa Mista Ayodele Olawande, masanin cigaban al'umma…
Read More
An mayar da Hukumar Rijistar ’Yan Ƙasa ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida

An mayar da Hukumar Rijistar ’Yan Ƙasa ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alamu na nuna cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta mayar da Hukumar Kula da Rijistar ’Yan Ƙasa (NIMC) daga Ma’aikatar Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Zamani ta Tarayya zuwa Ma’aikatar Kula Da Harkokin Cikin Gida ta Tarayya. Majiyoyi a cikin Hukumar NIMC, waɗanda suka tabbatar da hakan ga manema labarai, sun ce, ko da yake ba a bayyana shi a hukumance ba, amma za a fitar da sanarwar a nan gaba. An tattaro cewa matakin mayar da hukumar zuwa ma’aikatar harkokin cikin gida shi ne don magance matsalolin da ke da nasaba da bayar da Lambobin Shaidar…
Read More