20
Sep
Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamna a Kano, ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP sannan ta ayyana Yusuf Gawuna na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka guda a ranar 18 ga Maris. Bayan kammala zaɓe Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Yusuf Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Yayin da ɗan takarar APC, Nasir Gawuna, ya taya Kabir ɗin murnar lashe zaɓen ita kuwa jam'iyyarsa ta APC garzayawa kotu ta yi don ƙalubalantar sakamakon zaɓen. Yayin zaman yanke hukuncin da kotun ta yi a ranar Laraba, alƙalan kotun sun ba…
