Editor

9513 Posts
SERAP ta maka Tinubu a kotu kan tsoffin gwamnonin da ya naɗa ministoci suke karvar fansho

SERAP ta maka Tinubu a kotu kan tsoffin gwamnonin da ya naɗa ministoci suke karvar fansho

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Kare Haƙƙin 'Yan Ƙasa da Tabbatar da Shugabanci Nagari a Nijeriya (SERAP), ta kai ƙarar Shugaba Bola Tinubu kotu kan gazawarsa wajen hana tsofaffin gwamnonin da suke riƙe da muqamin minista karɓar kuɗaɗen fansho na jihohi. Ƙungiyar SERAP dai na neman kotu ta tilasta wa Tinubu ya umarci waɗannan tsofaffin gwamnonin da su daina karvar irin waɗannan kuɗaɗe. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Kolawole Oluwadare, ya ce ministocin da abin ya shafa su ne Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola. Sauran…
Read More
Tinubu na son karkatar da hankalin ‘yan Nijeriya su manta matsin rayuwar da suke ciki – Atiku

Tinubu na son karkatar da hankalin ‘yan Nijeriya su manta matsin rayuwar da suke ciki – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Litinin ne ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin ƙaddamar da tsarin farfaganda a cikin kwanaki masu zuwa. Ya yi nuni da cewa, Tinubu ya riga ya naɗa mataimakansa a kafafen yaɗa labarai sama da 15 da nufin tura munanan bayanai a matsayin tsarin mulkin ƙasa da kuma kawar da hankalin ‘yan Nijeriya daga matsanancin zafin da gwamnatinsa ta jawo musu. Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na Atiku, Phrank Shaibu, a cikin wata sanarwa,…
Read More
Za mu tabbatar da fannin ilim Zamfara na samun kaso mai tsoka daga kasafin jihar – Gwamna Lawal

Za mu tabbatar da fannin ilim Zamfara na samun kaso mai tsoka daga kasafin jihar – Gwamna Lawal

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bai wa fannin ilimin jihar muhimmaci ta hanyar ware masa kaso mai tsoka daga kasafin jihar na shekara-shekara. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron bikin maraba da sabbin ɗalibai wanda kwalejin Zamfara College of Arts and Science (ZACAS) da ke Gusau ta shirya a ranar Larabar da ta gabata. Mai magana da yawun Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ya ce taron ya gudana ne a harabar Kwalejin da ke Gusau, babban birnin jihar. Ya ƙara da cewa, Zamfara College of Arts and…
Read More
Da Dumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban jami’a a Zamfara

Da Dumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban jami’a a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A daren Alhamis da ta gabata wasu 'yan bindiga suka yi dirar mikiya a yankin Sabon Gida a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu ɗaliban Jami'ar Tarayya da ke Gusau (FUGUS) waɗanda ba a kai ga tantace yawansu ba. An ce ɗaliban da lamarin ya shafa na zama ne a wajen Jami'ar. Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida ma wakilinmu ta waya cewar, maharan sun shiga wurin kwanan ɗalibai guda uku inda a nan suka kwashi ɗaliban. “Yanzu da nake zancen nan da kai,…
Read More
Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar hana fita

Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar hana fita

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano da ya janye dokar hana zirga-zirga da aka sa biyo bayan sanar da hukuncin kuton sauraren zaɓen Gwamnan jihar Kano. Da yake sanar da umarnin, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya ce za a janye dokar ne saboda zaman lafiya da aka samu a jihar. Ya ƙara da cewa, janye dokar zai ba wa al'umma damar ci gaba da gudanar da alamuransu na yau da kullum kamar yadda aka saba. "Janye dokar za ta bai wa zai…
Read More
Da amincewar ma’aurata na ɗaura masu aure duk da ɗayansu na ɗauke da cutar HIV – Korarren Hakimi

Da amincewar ma’aurata na ɗaura masu aure duk da ɗayansu na ɗauke da cutar HIV – Korarren Hakimi

Daga UMAR GARBA a Katsina Jama'a na ci gaba da ce-ce-ku-ce kan dakatar da basaraken gargajiya a Katsina da gwamnatin jihar ta yi, saboda zarginsa da gwamnatin ta yi na ɗaura auren wasu ma'aurata biyu inda ɗaya daga cikinsu na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki. Gwamnatin jihar ta ce binciken da ta yi kan lamarin ta gano Alhaji Abubakar Abdullahi Ahmadu (Sarkin Kurayen Katsina), Hakimin gundumar Kuraye, ya karya dokar yin gwaji tsakanin wasu masu niyyar yin aure lamarin da ya sa gwamnatin ta tuɓe masa rawani. Sai dai basaraken ya bayyana wa manema labarai cewar da amincewar…
Read More
Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

"Ilimin 'ya mace har mijinta ke amfana" Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Kamar kowanne mako, shafin Gimbiya na yi maku tanadi na musamman wanda muke da tabbacin mata za su amfana ta vangarori da dama, ya Allah ya zama ƙwarin gwiwa ga wasu, wasu ya zama ilimi da zai taimaka masu wurin miƙewa neman na kai, yayin da yake zama allon kwaikwayo don saisaita rayuwarsu bisa ga turba da za ta tsirar da su. A wannan satin, mun samu baƙuncin wata matashiya da ta ɗauki sana'a da muhimmanci, mai sana'ar 'yankunne ce,…
Read More
Hukuncin Kotu: Za mu ƙwato ‘yancinmu a Kotun Ɗaukaka Ƙara – Gwamna Yusuf

Hukuncin Kotu: Za mu ƙwato ‘yancinmu a Kotun Ɗaukaka Ƙara – Gwamna Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce za su ɗukaka ƙara domin ƙwato 'yancensu. Kszalika, yi kira ga al'ummar jihar da a zauna lafiya, tare da shan alwashin zai yi amfani da hanyar shari'a wajen maido da nasarar da aka ƙwace masa. Manhaja ta rawaito a Larabar da ta gabata Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Kano ta yanke hukunci kan shari'ar da ke gabanta inda ta ce Yusuf Gawuna ne zaɓaɓɓen Gwamnan Kano amma ba Yusuf Kabir ba. Kotun ta bada umarnin a janye shaidar lashe zaɓen da aka bai wa Abba Kabir na Jam'iyyar NNPP sannan a miƙa…
Read More
An kafa dokar hana fita a Kano bayan yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar

An kafa dokar hana fita a Kano bayan yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kafa dokar hana zirga-zirga na sa'o'i 24 a faɗin jihar. Cikin sanarwar da ta fitar ranar Laraba ta bakin Kwamishinanta, rundunar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da kiyaye doka a faɗin jihar. Sanarwar ta ce al'ummar Kano su sani cewar, an riga da an tura jami'an da suka dace a sassan jihar domin tabbatar da an yi wa dokar hana zirga-zirgar biyayya. Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya ce dokar ta fara aiki ne daga ƙarfe 6 na yamma na ranar Laraba, 20…
Read More
Mu kula da rayuwar ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Mu kula da rayuwar ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga ’y’ya maza, inda yake da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau. Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi…
Read More