Mu kula da rayuwar ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga ’y’ya maza, inda yake da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau. Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi sani da karuwai ba, saboda dama su tuni sun fitsare ƙafafunsu, iyaye da sauran al’umma an sallama musu, saboda da salon rayuwar da suka ɗauka.

Sai dai abin takaici ne sosai, ka ga yarinya budurwa da ke zaune a gaban iyayen ta, kuma ta ke samun kulawa da tarbiyya ta shiga irin wannan mummunar rayuwa, da sani ko ba da sanin iyayen ta ba, wato kenan tana ɓoyewa iyayenta da waɗanda suka san ta, don kada su fahimci ta sauka a layi.

Idan a baya ya kasance abin kunya da takaici to, a yanzu sai dai ya zama abin assha da ya kamata kowa ya qyamace shi. Ba lallai ne kowa ya yarda ba, amma ni na san ’yan matan da yanzu suke shan wiwi da sauran sinadarai masu bugarwa da sa maye, fiye da maza, kuma ƙwaƙwalwarsu ta na ɗauka caraf, abin ya wuce yadda ake tsammani. Akwai wacce ma idan ta matsa sholisha a dankwalinta, sai a hankali.

Wani masanin lafiyar ƙwaƙwalwa Aliyu Alƙasim Yahuza ya bayyana cewa, akasari matasa suna shaye-shaye ne a saboda dalilai biyu, dalilin jin daɗi kamar yadda matasa ke yayin shan Shisha da wasu ke ganin ba komai ba ce, ko kuma sigari da wasu ke ɗaukar ta kamar ado. Sai kuma dalilin da ya shafi ƙoƙarin kawar da wata damuwa ko neman cajin ƙwaƙwalwa, don yin wasu ayyuka na fasaha ko karatu.

Da yawan matasa, mata da maza sun ɗauki ɗabi’ar yi wa maganin tari da mura shan wuce lissafi ne saboda yadda suke son sauya rayuwarsu zuwa irinta wasu ’yan gaba da fatiha da suke yi wa kallon sun waye, ko kuma su yi rayuwa irin ta abokai ko makusantansu ko domin kaucewa damuwa. Kamar yadda wata matashiya ta taɓa gaya min cewa, tana fita ta sayi maganin tari da mura ba da sanin iyayen ta ba, don ta sha ta samu yin barci mai nauyi, saboda ta kaucewa yawan tunane-tunane da ta ke yi cikin dare a dalilin rashin samun aure da wuri.

Wata marubuciya daga Jihar Kano, Rahama Sabo Usman ta haɗu da wata ɗalibar Islamiyya mai qwazo da natsuwa wacce a dalilin rashin gata da rasuwar mahaifinta, ta fara tallan wainar gero inda a ta wannan hanyar ce ta gamu da wani saurayi mai halayyar shaye-shaye wanda ya riƙa nuna mata kulawa da soyayya har ya ja hankalinta kan yadda za ta fita daga damuwar da ta ke ciki, wannan shi ya jefa rayuwar wannan yarinya cikin muguwar rayuwar da ta yi sanadin mutuwar ta a wani mummunan yanayi.

Bincike ya nuna cewa mutane na shiga harkar shaye-shaye ne kan dalilai daban daban da suka haɗa da, shan magani ba da izinin likita ba, inda sau da dama mutane kan da sun ji rashin lafiya sai su wuce kai-tsaye zuwa Kemis su sayo magani su fara sha ba tare da likita ya gwada su ya tabbatar da abin da ke damunsu ko irin maganin da ya dace su sha ba.

Rashin amfani da magani a kan ƙa’idar da aka ɗora mu shi ma wata hanya ce ta fara koyon shaye-shaye. Misali an ce ka yi sati ɗaya kana sha, sai ka yi kwana uku, ko kuma ka zarce adadin kwanakin da aka ƙayyade maka. Ko kuma an ce ka sha cokali ɗaya sai kai kuma ka sha rabin kwalba.

Matsalar bai wa yara rashin kulawa daga ɓangaren iyaye, inda za ka ga wasu iyayen basu damu da jan ’ya’yan su a jiki ba, har su san damuwarsu, irin wannan yana kawo matsalar da a Turanci ake kira ‘depression’, a bisa nazarin masana halayyar ɗan Adam. Kuma hakan har wa yau ya zo daidai da fahimtar wata malamar makaranta Aishatu Suleiman Abubakar da ke Jos da marubuciya Rahama Sabo Usman da ke Kano, waɗanda ke ganin lalacewar tarbiyyar iyaye ne ke jawo wa, saboda rashin jan yaransu a jiki da ba su fuskar da za su amayar da damuwarsu ko neman shawara.

Sannan kuma ana iya samun wannan matsalar a tsakanin ma’aurata da suke samun matsala ta fahimtar juna a tsakanin su, rashin samun waɗanda za su nemi shawara a wajen su ko yawan zurfin ciki, na daga cikin abin da zai sa wasu matan su fara shaye-shaye. Sakamakon yadda mijinta, kishiyarta, ’ya’yan miji ko wasu abokan zama suke ƙuntata mata, ko sun tsangwami rayuwar ta, ta yi ƙoƙarin sanar wa iyaye ko makusantan ta halin da take ciki an kasa fahimtar halin da take ciki. Daga nan ne sai ka ga mata ta fara nemarwa kanta mafita tana shaye-shaye, don ɗauke hankalinta daga damuwar da ke cinta a rai. Wata kuma tana fara wa ne da shan magungunan ƙarin kuzari don ta samu zafin naman yin aikace-aikacen gida nata ko na mutanen da take yi wa aikatau, daga nan kuma in jiki ya saba sai a zarce da harka.

Mu’amala da ƙawaye ko abokan zama na cikin gida masu shaye-shaye a ɓoye shi ma yana janyo yawaitar wannan matsalar da bazuwar ta a cikin al’umma ba tare da an ankara ba. Wasu iyaye mata suna da sakacin shan magani barkatai idan suna da ciki, wanda hakan na iya tava jinjiri kafin ma ya zo duniyar an koyar da shi. Ko kuma mata masu ajiye magani barkatai a ko’ina suka ga dama, har yaro ya ɗauka ya fara sha ba tare da an lura ba.

Har wa yau, an gano cewa wani lokaci likitoci kansu suna janyo wanan matsalar ta hanyar haɗa mutum da maganin da jininsa ba zai iya ɗauka ba. A hankali kuma sai jikin mutum ya saba har ya ajiye kwalin maganin ko takardar likita ya riqa zuwa Kemis yana saye, ko da bayan ya samu lafiya.

Na haɗu da mutane da dama, waɗanda a zahiri idan ka gansu cikin karamci da sutura ta mutunci ba za ka tava yi musu tunanin suna suna shaye-shayen magungunan ƙara kuzari da ɗauke damuwa ba. Kamar yadda wata abokiyar aiki da nake girmamawa ta tava yi min tayin shan wasu ƙwayoyi masu saurin ɗauke gajiya da sa a ji garau, bayan wani aikin rangadi na zagayen duba wasu ayyuka da muka yi. Saboda a ganinta shaye-shayen ƙwayoyin maganin cire gajiya ba wani abin damuwa ba ne, abu ne da ya zama gama gari, kuma ita ta saba, sai ta sha take barci.

Waɗannan su ne hanyoyin na daga cikin sanannun dalilan da ke hadddasa matsalar shaye-shaye a cikin al’umma. Kuma duk da ƙoƙarin da Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi, na faɗakarwa da kama masu kasuwancin wannan harka a birane da lunguna, abin kullum sai qara ta’azzara yake yi.

A wani bincike da tashar BBC ta gudanar a cikin shekarar 2019 a jihohin Kano, Legas, Jigawa da Kwara an gano yadda matasa, samari da ’yan mata a Nijeriya suka mayar da shan kodin ya zama kamar leda, inda za ka gansu sun tsuma shi a robar lemon kwalba na Coca Cola ko Lacasera suna tafiya suna sha a titi babu wani tsoro ko fargabar wani abu. Da yadda manyan kamfanonin haɗa magunguna ke haɗa baki da manyan dillalan irin waɗannan magunguna masu sa maye da bugar da hankali, ana kasuwancin su ta ɓarauniyar hanya ba tare da sanin hukumomi ba.

Abdullahi Kwamanda wani mai aikin banga ne da taimakawa jami’an tsaro a cikin anguwanni da ke Jos a Jihar Filato ya bayyana min irin yadda suka taɓa gano wata matar aure a cikin gidan mijinta tana cinikin kayan maye da tabar wiwi, ba tare da sanin mijinta ba. Kamar yadda wani rahoto ya bayyana ƙoƙarin da wasu jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Kano suka yi na gano wata mata da ke dillancin kayan shaye-shaye tana shiga gida-gida tana tallansu kamar goro.

Babu shakka wannan shaye-shaye da ’yan mata da matan aure ke yi yana kawo ƙaruwar mutuwar aure da ake kokawa a kai, da sanya yaran mata shiga harkar karuwanci da bin maza. Wani lokaci kuma da yawan shiga rikici da mutane ko cin zarafin wasu ba tare da tunanin komai ba, saboda rayuwa cikin maye. Akwai kuma batun tavarvarewar tarbiyar yara da yawan shiga rikici. Ashe wannan zai nuna nana cewar matsalar shaye-shaye ba ƙaramar matsala ba ce ga rayuwar mu da zamantakewar iyalin mu, da al’umma baki ɗaya.

Wasu yaran mata, Zainab Bala ’yar jarida, da Aeeshat Abdulhamid Isma’il shugabar Gidauniyar Tallafawa Mata ta Sisters Support Foundation sun koka da yadda wannan mummunar halayya ta shaye-shaye a tsakanin mata ke mayar da rayuwar mata baya da lalata musu tarbiyya, a matsayin su na iyayen al’umma.

Sun kuma bayyana buƙatar samar da cibiyoyin faɗakarwa da wayar da kai, da za a riqa qoqarin dawo da irin waɗannan matasa kan hanya madaidaiciya, domin gyara goben su, a matsayin su na ’yan Adam, da kuma lahirar su a matsayin su na Musulmi. Yayin da marubuciya Rahama Sabo ke ganin akwai buƙatar cibiyoyin ilimi suka ƙara mayar da hankali wajen buɗe ofisoshin ba da shawarwari ga ɗalibai na Guidance and Counseling, domin taimakawa matasa ɗalibai masu halayyar shaye-shaye.

Malam Aliyu Alƙasim kuma ya sake ƙarfafa gwiwar gwamnati kan masu harkar sayar da kayan Shisha da a kafa musu wata doka da za ta tilasta su sanya wasu alamu ko hotuna da ke sanar da masu sha cewa rayuwar su na cikin haɗari, in suna ci gaba da shan wannan abin, kamar yadda aka yi wa masu kamfanonin yin taba sigari. Sannan malamai da masu faɗakarwa a ci gaba da ƙoƙarin wayar da kai don ganin an raba matasa da wannan mummunar rayuwa.