Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ce Yusuf Gawuna ne zaɓaɓɓen Gwamnan Kano

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamna a Kano, ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP sannan ta ayyana Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka guda a ranar 18 ga Maris.

Bayan kammala zaɓe Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Yusuf Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Yayin da ɗan takarar APC, Nasir Gawuna, ya taya Kabir ɗin murnar lashe zaɓen ita kuwa jam’iyyarsa ta APC garzayawa kotu ta yi don ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Yayin zaman yanke hukuncin da kotun ta yi a ranar Laraba, alƙalan kotun sun ba da umarnin a janye shaidar lashe zaɓen da aka miƙa wa Yusuf Kabir sannan a miƙa wa Gawuna.

Kotun ta zabtare ƙuri’u 165,663 daga adadin ƙurin da Gwamna Yusuf a matsayin ƙuri’u mara amfani sakamakon ba su ɗauke shaidar kan sarki ko rataɓa hannun hukuma.