Editor

9513 Posts
Kotu ta ayyana Alia a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Binuwai

Kotu ta ayyana Alia a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Binuwai

Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Jihar Binuwai mai zamanta a Makurdi, ta tabbatar da Gwamna Hyacinth Alia na Jam'iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar. Kotun ta kuma yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Titus Uba, suka shigar inda suke ƙalubalabtar sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a ranar 18 ga Maris. Shugaban alƙalan kotun, Mai Shari'a Ibrahim Karaye, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar kasancewar ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar mata abu ne da ya shafi gabanin zaɓe kamar yadda yake ƙunshe a Sashe na 285 ns Dokar Zaɓe. Kotun ta ce…
Read More
An kori babban sakataren hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya

An kori babban sakataren hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafar Sifaniya ta kori babban sakatarenta Andreu Camps tare da neman afuwa kan abin da ya faru bayan wasan ƙarshe na cin Kofin Duniya na mata. Hukumar ta ce, ta hanzarta yi wa tsarinta garambawul domin cika alƙawarin da ta yi wa 'yan wasa. Tun da farko, mafi yawan 'yan wasan sun amince da su kawo ƙarshen kaurace wa tawagar ƙasar. 'Yan wasan sun fara ƙaurace wa tawagar ne bayan tsohon shugaban hukumar Luis Rubiales ya sumbaci 'yar wasa Jenni Hermoso lokacin nasarar da Sifaniya ta samu a kan Ingila a wasan ƙarshe na…
Read More
Nijeriya na ƙara kwarjini a idon duniya ƙarƙashin Tinubu – Ministan Labarai

Nijeriya na ƙara kwarjini a idon duniya ƙarƙashin Tinubu – Ministan Labarai

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Ministan Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, Nijeriya na qara kwarjini samun tagomashi da kwarjini a idon duniya ƙarƙashin kyakkyawan jagorancin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake bai wa ƙasar. Ministan Labaran ya bayyana hakan ne jiya a tattaunawar da ya yi da Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA) a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ake gudanarwa a New York dake Amurka, inda ya ƙara da cewa, Shugaban Nijeriyar ya ƙara fito da martabar ba wai kawai Nijeriya ita kaɗai ba, a’a, har ma da Nahiyar Afrika bakiɗaya. “Ziyara ce mai…
Read More
NLC ta bayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani

NLC ta bayyana shiga yajin aikin sai baba-ta-gani

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan gazawar gwamnati wajen cimma buƙatunta. Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na NLC, Benson Upah, shi ne ya bayyana shiga yajin aikin a ranar Juma'a. Tun da fari, sai da NLC ta yi yajin aiki na kwana biyu a matsayin gargaɗi ga gwamnati, sannan daga bisani ta bai wa gwamnatin wa'adin mako biyu na gwamnati ta yi abin da ya kamace ta. Wa'adin mako biyun ya ƙare ne a ranar Juma'ar da ta gabata, ba tare da gwamnatin ta biya buƙatun NLC ɗin ba don…
Read More
Mohbad: Dalilinmu na harba barkonon tsohuwa a Lekki – ‘Yan Sanada

Mohbad: Dalilinmu na harba barkonon tsohuwa a Lekki – ‘Yan Sanada

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana a ranar Juma'a cewa, ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa taron jama'a da aka haɗa a babbar ƙofar gari a Lekki a ranar Alhamis. Rahotanni sun ce jama'a sun yi dandazo a yankin ne don nuna alhini da kuma jana'izar mawaƙin nan Ilerioluwa Oladimeji Aloba (Mohbad) a Victoria Island, Legas. A cewar mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, “Babu harsashi ko guda da aka harba. 'Yan sanda sun yi amfani da salon tattalin irin taron jama'ar da aka haɗa ba bisa doka ba. “Ba a samu asarar rai ba,…
Read More
Wike ya ƙwace filayen su Peter Obi a Abuja

Wike ya ƙwace filayen su Peter Obi a Abuja

A wani mataki na yin aiki ba sani ba sabo da Ministan Abuja, Nyesom Wike, yake yi don gyara wa birnin tarayya zama, Ministan ya ƙwace wasu filaye a birnin mallakar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyya Labour (LP) a babban zaɓen 2023, Peter Obi da tsohon Gwamnan Kuros Riba Liyel Imoke. Sanarwar da Babban Sakataren Hukumar Abuja, Olusade Adesola, ya fitar a ranar Alhamis ta nuna filayen Obi da na Imoke na daga cikin fuloti 165 da ministan ya janye mallakarsu ta dawo hannun gwamnati. A cewar sanarwar, Wike ya ƙwace filayen ne sakamakon mamallakansu sun ƙi gina su.…
Read More
Garkuwa da ɗalibai a Gusau: Gwamnan Zamfara ya kira taron gaggawa da majalisar tsaro

Garkuwa da ɗalibai a Gusau: Gwamnan Zamfara ya kira taron gaggawa da majalisar tsaro

An ceto ɗalibai shida tare da kashe ‘yan bindiga da dama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kira taron gaggawa na Majalisar Tsaron Jiha, biyo bayan sace ɗaliban Jami’ar Tarayya dake Gusau. Wannan taron gaggawan an kira shi ne saboda ɗaliban da aka sace a muhallinsu dake wajen jami’a, a Ƙauyen Sabon Gida na ƙaramar Hukumar Bungudu. A wata sanarwar manema labarai, wacce mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau Juma’a, ta ce an kira taron gaggawan ne domin tabbatar da ganin an ceto dukkanin waɗanda aka sace, tare kuma da bin hanyoyin kawo ƙarshen matsalar…
Read More
NNPCL ya yi wa wasu shugabannin kamfanin ma’aikatansa ritayar dole

NNPCL ya yi wa wasu shugabannin kamfanin ma’aikatansa ritayar dole

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rarraba man fetur a Nijeriya (NNPCL) ya yi wa wasu daga cikin manyan ma'aikatansa/ shugabannin kamfanin ritayar dole. Wato ya tilasta wa wasu manyan ma'akatansa da wa'adin yin ritayar aikinsu ba ta wuce nan da watanni 15 masu zuwa ba yin ritayar dole. Wannan jawabin yana ƙunshe ne a cikin wani jawabi da hukumar gudanarwar ta kamfanin ta bayar a ranar Litinin ɗin da ta gabata ranar 18 ga Satumba, 2023, sannan ta wallafa a asusunta na shafin X (wanda da aka fi sani da Tiwita) a safiyar ranar Talata. Hakazalika, sanarwar ta bayyana cewa,…
Read More
Hukumar FBI ta Amurka na neman wasu ‘yan Nijeriya shida ruwa a jallo

Hukumar FBI ta Amurka na neman wasu ‘yan Nijeriya shida ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ‘yan Nijeriya shida sun tsinci kansu a cikin tsaka-mai-wuya na hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI), inda hukumar ta ayyana su a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo da kuma haɗari na ƙasa da ƙasa. Waxanda ake zargin sun haɗa da Felix Osilama Okpoh, Alex Afolabi Ogunsakin, Micheal Olorunyomi, Richard Izuchukwu Uzhi, Nnamdi Orson Benson, da Abiola Ayorinde Kayode. FBI ta kira su “wanda aka fi so a cyber.” A cewar FBI, wanda ake nema sextuplet “a halin yanzu yana zaune a Nijeriya.” Hukumar FBI ta yi kira ga jama’a da…
Read More
’Yan wasan da suka fi ɗaukar katin gargaɗi a duniyar ƙwallon ƙafa

’Yan wasan da suka fi ɗaukar katin gargaɗi a duniyar ƙwallon ƙafa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Katin gargaɗi wato ‘Yellow Card’ kati ne wanda alƙalin wasa yake bawa ɗan wasa domin ya rage duka da sauran wasu ɗabi’u da basu kamata ba yayin da ake fafata wasa a tsakiyar fili. Akwai wasu ’yan wasa guda biyar da tarihin katin gargaɗi bazai taɓa mantawa da su ba har kawowa iyanzu. Ga jerin sunayen ’yan wasan da suka fi ɗaukar katin tun daga na 1 har zuwa na 5. Sergio Ramos: Sergio Ramos Garcia ɗan wasan ƙasar Sifaniya wanda yake fafata wasan sa a Paris saint-german da tawagar ƙasar Spain. Yana doka wasan sa…
Read More