Editor

9513 Posts
Shugabancin Legas: Gwamna Sanwo-Olu ya yi nasara a kotu

Shugabancin Legas: Gwamna Sanwo-Olu ya yi nasara a kotu

Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamna a Jihar Legas, ta tabbatar da Gwamna Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Da yake karanto hukuncin a madadin sauran alƙalan yayin zaman kotun a ranar Litinin, Mai Shari'a Mikail Abdullahi ya ce ƙarar da Jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Olajide Adediran, suka shigar ba ta da daraja wanda hakan ne ya sa kotu ta kori ƙarar. Tuhumar da ake yi wa Gwamnan Sanwo-Olu ta haɗa da amfani da takardun bogi da kuma cewa jam'iyyarsu ta APC ba ta tsayar da shi da mataimakinsa takara bisa ƙa'ida ba. Bayan sauraren duka…
Read More
Adamu Ibrahim Wanki ya zama Daraktan Ma’aji na FCTA

Adamu Ibrahim Wanki ya zama Daraktan Ma’aji na FCTA

An naɗa Alhaji Adamu Ibrahim Wanki a matsayin sabon Daraktan Ma'aji na Hukumar Birnin Tarayya, Abuja. Wanki ya zama sabon Daraktan ne biyo bayan ritayar da mai riƙe da muƙamin, Alhaji Zanna Hamza, ya yi a sakamakon cika shekara 60 da ya yi a bakin aiki. Bikin miƙa ragamar ofishin ya gudana ne a babban zauren taron sashen tsarin tattalin arziƙi da ƙididdiga na FCTA da ke area 11, Abuja. Taron ya samu halartar daraktoci na sassa daban-daban haɗi da sauran jami'an FCTA. Kafin naɗin nasa, Alhaji Adamu Ibrahim Wanki shi ne jami'i mafi girma a sashen nasu. Sashen ma'ajin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a Kotun Ƙoli a Abuja

Da Ɗumi-ɗumi: Gobara a Kotun Ƙoli a Abuja

Bayani da ɗumi-ɗumi da muka samu da safiyar Litinin ya nuna cewa, gobara ta tashi a wani sashen ginin Kotun Ƙoli da ke Abuja. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari ba a kai ga ayyana dalilin tashin gobarar ba. Amma a hango wasu ma'aikata yayin da suke ta ƙoƙarin kawar da kayayyaki a wasu sassn ginin gudan kada gobarar ta shafe su. Kazalika, an ga jami'an kwana-kwana sun ba da himma wajen kashe gobarar. Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da 'yan takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyun PDP da LP, wato Atiku Abubakar da Peter Obi, suka shigar…
Read More
Masu garkuwa sun ɗauki salon ɗauki-ɗaiɗai a Kebbi 

Masu garkuwa sun ɗauki salon ɗauki-ɗaiɗai a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Masu garkuwa da mutane sun ɗauki sabon salo a waɗansu sassan Jihar Kebbi, inda yanzu a maimakon kai hari da suke yi a baya a cikin ayarin babura masu yawa, sun ɗauki salon ɗauki-ɗaiɗai, inda suke shiga cikin gari da tsakar dare su ɗauki mutum ɗaya ko biyu zuwa biyar maimakon ayarin mutane. Yankin ƙananan hukumomin Koko/Besse, Bagudo da Maiyama dai yanzu a nan ne waɗannan mutanen ke cin karensu ba babbaka duk da irin ƙoƙarin da hukumomin tsaro da ’yan sa-kai ke yi. A cikin daren ranar Larabar da ta gabata waɗannan mutanen sun…
Read More
Sulhu da ‘yan bindiga: Gwamnan Zamfara ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta gudanar da bincike

Sulhu da ‘yan bindiga: Gwamnan Zamfara ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta gudanar da bincike

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙwaƙƙwaran bincike kan sulhu da da ake yi da ‘yan bindiga a jihar. Rahotonni sun bayyana yadda wata tawaga ta Gwamnatin Tarayya take gudanar da zaman sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara, ba tare da sanin Gwamnatin Jihar ba. A wata sanarwa wacce mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar litinin, gwamnatin ta Zamfara ta yi Allah wadai da tawagar ta Gwamnatin Tarayya wacce take jagorantar wannan sulhu, tare da alhinin cewa ko tuntuɓar gwamnatin jihar ba a yi…
Read More
Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Illar gurɓata muhalli ga rayuwar al’umma

Rahotanni daga Hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) sun nuna cewa, aƙalla gurɓata muhalli na sanadiyyar salwantar rayukan kusan mutum miliyan goma a duniya a kowace shekara. Wani babban abin tashin hankalin shi ne Nijeriya na daga cikin ƙasashen Afirika da wannan matsala ta yi ƙamari a cikinta, kuma ita ce ta huɗu a cikin jerin ƙasashen duniya da ake fama da wannan matsala ta gurɓata muhalli. Domin kuwa ƙididdiga ta nuna cewa, duk cikin ’yan Nijeriya dubu ɗari, akwai mutum ɗari da hamsin da ke mutuwa sakamakon shaƙar gurɓatacciyar iska a kowace shekara. A ƙasar Afganistan mutum 406,…
Read More
An sauke wa acaɓa, keke napep farashin fetur zuwa N430 a Borno

An sauke wa acaɓa, keke napep farashin fetur zuwa N430 a Borno

An sauke farashin litar mai zuwa Naira 430 don amfanin 'yan acaɓa da matuƙa adaidaita-sahu da 'yan taksi a jihar Borno. Bayanai sun ce ƙaddamar da dogayen motoci guda 70 da gwamnatin jihar ta yi don rage raɗaɗin rayuwa inda jama'a kan biya N50, hakan ya sa sauran masu abubuwa na 'yan kasuwa a jihar kowa na neman matsaya. An ce wasu masu hannu da shuni a jihar suka bai wa gidajen mai a babban birnin jihar kwangilar sayar da fetur N430 kan kowace lita a maimakon N637. Bayanai sun ce masu hannu da shunin sun ɗauki wannan mataki ne…
Read More
Tinubu ya ba da umarnin ceto ɗaliban Gusau

Tinubu ya ba da umarnin ceto ɗaliban Gusau

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumomin tsaro umarni kan su gaggauta ceto ragowar ɗalibai mata na jam'iyyar tarayya da ke Gusau waɗanda 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su kwanan nan. Idan ba a manta ba, a ranar Juma'ar da ta gabata wasu 'yan bindiga suka bi ɗaliban har ɗakunan kwanasu suka sace su. Sa'o'i kaɗan da faruwar lamarin rundunar tsaro ta haɗin gwiwa, wato Hadarin Daji, mai yaƙi da matsalolin tsaro a yankin, suka samu nasarar kuɓutar da mutum shida daga cikin ɗaliban da aka yi awon gaba da su. Umarnin na Tinubu na ƙunshe ne…
Read More
Rana ko iska a matsayin makamashi

Rana ko iska a matsayin makamashi

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI Batunmu na wannan makon shine, hasken rana da kuma iska a matsayin sinadiran da za su samar da makamashi da zai samar da wutar lantarki ga gidajenmu da ofisoshinmu da guraren gudanar da sana’oi da suke buƙatar wutar lantarki har da masana’antu da suke buƙatar wutar lantarki har da masana’antu da kamfanoni da gonaki, kai da duk wuni guri da ake buƙatar wutar lantarki. Kimiya, wato Ilimin ƙwaƙwa da na ci da kuma zurfafa tunani kan al’amari mai tafiya da kuma komowa, sai kuma ilimin fasaha wato, ilimin sarrafa abubuwa zuwa wani abun. Ɗan Adam…
Read More
Tsaro: Gwamna Dauda Lawal ya haramta haƙar ma’dinai ba bisa ƙa’ida ba a Zamfara

Tsaro: Gwamna Dauda Lawal ya haramta haƙar ma’dinai ba bisa ƙa’ida ba a Zamfara

*Ya umurci jami’an tsaro su ɗauki tsattsauran mataki A yau Asabar, Gwamnan Dauda Lawal, ya sanar da haramta haƙar ma’idanai ba bisa ƙa’ida ba, tare da umurtar jami’an tsaro su ɗauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka kama yana aikata hakan. A tsawon shekaru, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na daga cikin abubuwan da ke ta’azzara harkar ‘yan bindiga a faɗin Jihar Zamfara. Gwamna Lawal, a wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki wannan matakin ne domin daƙile wannan ɓarna ta haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba,…
Read More