Editor

9513 Posts
In rabonka ne zai zo har gabanka ne

In rabonka ne zai zo har gabanka ne

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Taken wannan rubutun nawa ya fito ne daga baitukan wata waƙa da wani mawaƙin Hausa hip hop ɗan Jihar Gombe mai suna S. Nigga ya gabatar a gaban dafifin mahalarta taron Tedx Pantami, wanda wasu matasa a jihar suka shirya da nufin tattauna wasu matsaloli da suka addabi al'ummar Arewa, musamman mazauna Jihar Gombe. Har wa yau kuma a samar da mafita wanda gwamnati da al'umma za su yi aiki da su, don samar da canji a rayuwarsu. Taron, wanda nima na samu damar halarta a matsayin gayyata ta musamman daga masu shiryawa, ya samu…
Read More
Da me matan banza suka fi na gida?

Da me matan banza suka fi na gida?

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafin zamantakewa a jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Yau zan so mu tattauna wani batu mai matukar mahimmanci, wato dame matan banza su ka fi matan cikin gida? Wannan tambaya ce da matan aure kan yi wa mazaje don gano dalilin da ya sa suke bin matan banza. Bayan ga su nan a gida, ba abinda suka rasa na halitta ko kyautatawa. Gaskiyar magana, da yawa matan waje sun fi na cikin gida ta fuskoki da dama. A biyo ni a hankali don tattauna waɗannan batutuwa: Kwalliya/Ado: Matan waje ba…
Read More
Kotu mai matakai uku, Abba zai shiga uku

Kotu mai matakai uku, Abba zai shiga uku

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A Hausa in an ce mutum "YA SHIGA UKU" a na nufin ya shiga garari da sai yadda hali ya yi a samu a ceto shi ko ya kuɓuta daga damuwa. In an duba 3 a gurguje ka iya zama duwatsun murhu da duk wanda ya shiga tsakiyar su in ba tukunya ba to zai ji jiki ko za a yi abun nan da a ke cewa "Da kyar na tsira ya fi da ƙyar a ka kama ni." Amma abun na da ke son magana a nan shi ne damar ɗaukaka ƙara har matakai…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tabbatar da Yahaya a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Gombe

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta tabbatar da Yahaya a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Gombe

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Gombe ta tabbatar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Yayin zamanta a ranar Talata, kotun ta yi watsi da ƙarar da aka shigar inda ake ƙalubalantar nasarar lashe zaɓen da Yahaya ya yi. 'Yan takaran jam'iyyun hamayya a jihar, wato Jibrin Barde na PDP da Nafiu Bala na ADC, su ne suka shigar da ƙarar inda suka nuna rashin gamsuwarsu da sake zaɓen Inuwa Yahaya da Mataimakinsa, Manassah Daniel Jatau da aka yi a matsayin shugabannin jihar ƙarƙashin Jam'iyyar APC. Duka alƙalan kotun su uku, sun yi…
Read More
Yadda karyewar gada ta haifar da tsaiko ga zirga-zirgar jama’a a Inugu

Yadda karyewar gada ta haifar da tsaiko ga zirga-zirgar jama’a a Inugu

Karyewar gada a babbar hanyar Inugu zuwa Fatakwal a jihar Inugu, ta jefa al'ummar yankin cikin halin tsaiko. Karyewar gadar a ranar Litinin da ta gabata, ta haifar da tsaikon zirga-zirga ga masu amfani da hanyar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan Jihar Inugu, Dan Nwomeh, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X (Twitter). A cewar Nwomeh, gwamnati ta gargaɗi masu abubuwan hawa da su guji bin hanyar da ke tsakanin New Artisan da Naira Triangle a Jihar Inugu. Ya ƙara da cewa, jami'an gwamnatin tarayya da jihar sun hallara wurin don ɗaukar…
Read More
Ban yi zaton zama zakaran gasar ɗaukar hoto ta Wiki Loves Africa – Maikatanga

Ban yi zaton zama zakaran gasar ɗaukar hoto ta Wiki Loves Africa – Maikatanga

Daga AISHA ASAS Shahararren mai ɗaukar hoton nan da sunansa ya yi tambari a ƙwarewa ta vangaren samar da ingantattun hotuna, Malam Sani Mohammed Maikatanga, ya bayyana yadda ya ji yayin da ya samu tabbacin lashe gasar ɗaukar hoto ta Wiki Loves Africa, wanda ya bayyana cewa ba zato ba tsammani ya ji kansa a matsayin zakaran gasar. Ya kuma bayyana farin cikinsa kan cin gasar, wadda ke ɗauke da la'ada ta dalar Amurka 2,000. A satin da ya gabata ne Manhaja ta ruwaito cewa, gasar wadda ta ginu akan sauyin yanayin duniya, abinda bature ke kira da ‘Climate &…
Read More
Sulhu da ‘yan bindiga: Gwamna Dauda Lawal ya maida wa Ministan Labarai martani

Sulhu da ‘yan bindiga: Gwamna Dauda Lawal ya maida wa Ministan Labarai martani

*Muna da hujjojin da ke fallasa jami’an Gwamnatin Tarayya Gwamna Dauda Lawal yau Talata, ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga. A ranar Litinin da ta gabata Ministan na Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro. Biyo bayan neman ƙarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ƙarƙashin ƙasa da ‘yan bindiga. A wata takardar manema labarai, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa…
Read More
Yadda jarumin shirin ‘Daɗin Kowa’ ya zama furodusa

Yadda jarumin shirin ‘Daɗin Kowa’ ya zama furodusa

DAGA MUKHTAR YAKUBU Fitaccen jarumi a cikin shirin 'Dadin Kowa', Muhammad Usman wanda aka fi sani da Razaki a yanzu haka likkafar ta ci gaba inda ya shiga cikin matasan furodusan da suke tasowa a wannan lokacin. Domin kuwa a cikin satin da ya gabata ne ya saki fim ɗin sa mai suna 'Baban Ladi' a shafin sa na You Tube mai suna 'Yar AroTV wanda a kuma zuwa yanzu dubunan mutane suka kalli fim ɗin zuwa dan qaramin lokacin da aka fara saka shi. Domin jin yadda jarumin ya rikiɗe zuwa furodusa wakilinmu ya tambayi Razaki Dadin Kowa ko…
Read More
A yi biris da yadda Gwamnatin Zamfara ke siyasantar da matsalar tsaro – Minista

A yi biris da yadda Gwamnatin Zamfara ke siyasantar da matsalar tsaro – Minista

Gwamnatin Tarayya ta bayyana matuƙar damuwa kan wata sanarwa da ta fito daga Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal Dare. Gwamnatin ta ce maimakon gwamnan ya nuna jin daɗi da farin ciki ganin yadda jami'an tsaro da hukumomin Gwamnatin Tarayya ke ta ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Gusau daga hannun 'yan bindiga, sai ya maida matsalar siyasa don kawai ya cimma wani buri a siyasance. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka bayan ya nazarci yadda dokar ƙasa ta bai wa hukumomin Gwamnatin Tarayya ƙarfin ikon zabura domin ɗaukar…
Read More
Yadda Nijeriya ta ɗau saiti gadan-gadan a cikin gida da waje ƙarƙashin mulkin Tinubu

Yadda Nijeriya ta ɗau saiti gadan-gadan a cikin gida da waje ƙarƙashin mulkin Tinubu

Daga MOHAMMED IDRIS Nan a cikin gida, Shugaba Bola Tinubu ya kama aiki ka'in-da-na'in, ba tare da wani jinkiri ba, musamman manyan tsare-tsaren saita fasalin tattalin arzikin ƙasa. Baya ga wannan kuma, Shugaba Tinubu ya yi amfani da damar da ya samu a cikin watan Satumba, ya yi wa duniya shiga-da-ƙafar-dama. Satumba ne ya fi zama watan da ayyuka da sha'anin tafiyar da mulki su ka fi kacame masa a cikin duniya, tun bayan rantsar da shi. Shugaba Tinubu ya tafi Indiya inda ya halarci Taron Ƙasashe Masu Ƙarfin Tattalin Arziki na Duniya, wato G20. Shugaban Indiya, Modi, shi ne…
Read More