Yadda jarumin shirin ‘Daɗin Kowa’ ya zama furodusa

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Fitaccen jarumi a cikin shirin ‘Dadin Kowa’, Muhammad Usman wanda aka fi sani da Razaki a yanzu haka likkafar ta ci gaba inda ya shiga cikin matasan furodusan da suke tasowa a wannan lokacin.

Domin kuwa a cikin satin da ya gabata ne ya saki fim ɗin sa mai suna ‘Baban Ladi’ a shafin sa na You Tube mai suna ‘Yar AroTV wanda a kuma zuwa yanzu dubunan mutane suka kalli fim ɗin zuwa dan qaramin lokacin da aka fara saka shi.

Domin jin yadda jarumin ya rikiɗe zuwa furodusa wakilinmu ya tambayi Razaki Dadin Kowa ko ya aka yi hakan ta kasance? Inda ya fara da cewa, “to gaskiya wannan ba wani sabon abu ba ne idan ka dubi yadda harkar fim take a duniya, kuma ita ma masana’antar mu ta Kannywood duk haka abin yake, saboda duk wani jarumi da ya shahara a Kannywood za ka ga ya tava yi ko kuma yana yin furodusin.

“To ni ma idan ka kalli rayuwata ai ba da sharin ‘Dadin Kowa’ na fara fim ba. Na fito a finafinai da dama. Domin dai ka ga ni haifaffen garin Kano ne kuma duk karatuna a cikin garin Kano na yi har na zo na shiga cikin harkar fim domin na bayar da tawa gudunmawar.

“Kuma na fara a matsayin jarumi wanda har na zo nake ɗaukar nauyin shirin fim wanda zan ba mutane su yi ni kuma ina matsayin babban furodusa duk da yake dai finafinan da na yi ba su da yawa kuma haka a harkar aktin ma ban yi finafinai ba, na dai fara da ‘Dadin Kowa’, shi ya sa ma mutane suka fi sani na da shi, sai kuma wani fim da na fito a cikin sa a matsayin jarumi, mai suna ‘Kwana Bakwai’, sai kuma na fito a cikin fim din ‘Ya mace’ da ‘Tarkon Ƙauna’ Ina ganin waxannan finafinai guda huɗu su ne na fito a cikin su a matsayin jarumi.

“A yanzu kuma na sake sauya salo na dawo a matsayin furodusan da na shirya sabon fim ɗina mai suna ‘Baban Ladi’.”

Dangane da yadda aka shirya fim din ‘Baban Ladi’ kuwa cewa ya yi, “wato shi yanayin aikin ma ya bambanta da sauran aikin da na saba yi ko na saba gani domin ƙwarewar da na yi a wajen koyo da kuma ganin yadda a ke gudanar da aikin fim, shi ya sa da na tashi aikin fim ɗin ban yi masa shiri na wasa ba, don haka aiki ne da ya samu kulawa sosai da kuma bin tsarin da ya kamata a gudanar da aikin.”

A ɓangaren saƙon da fim ɗin ya ƙunsa kuwa cewa ya yi, “an zo da wani salo ne wanda ba irin yadda mutane suka saba kallo ba. Saboda haka fim ɗin ‘Baban Ladi’ ba na shakkar zai ba masu kallo mamaki, don haka ma bayan mun sake shi a You Tube a “Yar Aro TV muke raba shi ga masu turawa a waya domin saƙon ya shiga duk inda a ke buƙatar a kalla.

Saboda shi labarin na wata yarinya ne da take fafutukar neman ta yi ilimi wanda hakan ya sa take fuskantar qalubale iri-iri, har ta kai ga wani ya shigo yana ƙoƙarin ya taimake ta in da shi ma ya rinƙa samun kansa cikin matsala. Don haka fim ɗin yana ɗauke da barkwanci da kuma abubuwa da dama na faɗakarwa da nishaɗantarwa.”

Dangane da jaruman fim ɗin kuwa cewa ya yi, “ai domin aikin ya tafi cikin ƙwarewa, sai muka hafa tsofaffin jarumai da kuma sababbi, ta yadda su tsofaffi su nuna ƙwarewar su. Su kuma sababbi a ba su damar da su ma nan gaba za su ƙware. Kuma Alhamdulillahi ko a yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu daga yadda mutane suke ta shiga YouTube ɗin mu suna kallo kamar yadda na faɗa maka a baya cikin wannan satin dubunan mutane ne suka shiga suka kalla kuma za mu ci gaba da sakin shi a duk ranar Laraba.

“Don haka ni dai burina da wannan fim ɗin ya zama zakaran gwajin dafi in da zai zama a duk masana’antar Kannywood babu kamar sa yadda ko su ‘yan fim ɗin ma ya zama suna kafa misali da shi. Don haka Ina kira ga abokan sana’ata da mu dage mu yi aikin na gaskiya.”