Editor

9513 Posts
DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Ibrahim Musa

DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Ibrahim Musa

Hukumar tsaro ta DSS ta sako Editan Jaridar Almizan, Malam Ibrahim Musa, wanda da farko take tsare da shi. Ɗan uwan Editan, Abdullahi Usman ne ya sanar da hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Juma'a. Manhaja ta rawaito jami'an DSS sun tsare Ibrahim Musa a Babban Filin Jirgin Saman Aminu Kano da ke Kano da safiyar Larabar da ta gabata a lokacin da yake ƙoƙarin tafiya Umara a Saudiyya. Bayanai sun ce an sako Editan a ranar Alhamis, kuma an maida masa dukkan takardunsa na tafiya. Usman ya ce lafiya ƙalau Editan ya koma cikin ahalinsa da 'yan da…
Read More
An shiga ruɗani game da hukuncin kotu kan shari’ar zaɓen Gwamnan Kaduna

An shiga ruɗani game da hukuncin kotu kan shari’ar zaɓen Gwamnan Kaduna

Jama'a sun shiga halin ruɗani game da shari'ar zaɓen gwamna a jihar Kaduna. Hakan ya faru ne bayan da wani rahoto ya nuna Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe na Gwamnan Jihar ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba. Bayan kimanin awa guda da fitan rahoton, sai aka sake ganin wani rahoto na daban na cewa, kotun ta tabbatar da nasarar da Gwamna Uba Sani ya samu a zaɓen wanda hakan ke nuni da shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar. Da yake yi wa Jaridar News Point Nigeria ƙarin haske game da hukuncin ta waya, lauyan Gwamna Sani, Ibrahim H O…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ayyana zaɓen gwamnan Kaduna ‘Inconclusive’

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta ayyana zaɓen gwamnan Kaduna ‘Inconclusive’

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Kaduna, ta ayyana zaɓen gwamnan jihar da ya gudana ran 18 ga Maris a matsayin wanda bai kammala ba, wato 'inconclusive.' Kotun ta ayyana hakan ne a zaman yanke hukunci kan shari'ar da ta yi a ranar Alhamis. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Victor Oviawe ta bai wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, da ta gudanar da zaɓen cike giɓi a cikin kwana 90. Da wannan hukuncin, ana sa ran INEC ta sake shirya zaɓe a gundumomi bakwai a tsakanin ƙananan hukumomi huɗu kuma a rumfunan zaɓe 24 masu ɗauke da masu kaɗa ƙuri'a…
Read More
Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

"Samarin yanzu ma sun fi son mace mai sana'a" Daga AISHA ASAS Mai karatu yau fa mun zo da abinda ba ku yada gani ba, mace da ta tabbatar da zancen ba sana'ar da namiji zai yi da mace ba zata iya ba matuƙar ta sa wa ranta za ta iya. A daidai wannan lokacin da mata suka miƙe, suka yi tarayya wurin kama sana'ar kayan qawa na mata da maza, kama daga tufafi, takalma zuwa huluna, gyale da sauransu, waɗanda su ne sana'oin da aka cika ganin mata na yi. A cikin haka ne, aka samu wata matashiya da…
Read More
‘Janar’ Kawankwaso: Daga ina zuwa ina?

‘Janar’ Kawankwaso: Daga ina zuwa ina?

Daga MUKHTAR MUDI SIPIKIN Wani hatsabibin marubuci wato Robert Green wanda ya wallafa littafin "48 Laws Of Power" ya kawo wata saɗara mai muhimmanci da ke cewa; "The moment of victory is a moment of danger because you’re tempted to press your luck…" Bayan zaven 2015, Kwankwaso ya bunƙasa ya tumbatsa a siyasar Jahar Kano, ya zama Sanata, ya naɗa Gwamna da mataimakinsa, ragowar Sanatoci biyu wato Gaya da Barau dole sun yi masa bai'a sun bi, kai duk wata kujera tun daga 'yan Majalissa Jiha da na Tarayya duk nasa ne. Ya kai siyasar gidan Shekarau gargarar mutuwa. A…
Read More
Shari’ar siyasar Kano: Inda jami’yyar NNPP mai mulki ta kuskure

Shari’ar siyasar Kano: Inda jami’yyar NNPP mai mulki ta kuskure

Daga ABDULAZIZ TIJJANI BAQO A matsayina na ɗan NNPC kuma ɗan kwankwasiyya cikakke, ga mahangata a game da hukuncin da kotu ta yanke a kan shari'ar da ake tafkawa a tsakanin jam'iyyarmu ta NNPP da kuma APC. Bayan karanta kes ɗinmu da APC daga farko zuwa ƙarshe, ba ni da wani haufi a kan cewa lauyoyinmu su suka yi mana illa a wannan kes din. Sun yi iya bakin ƙoƙarinsu. Amma kuskuren da suka yi wurin laƙantar doka ya jawo mana matsala. Kusan gabaɗaya kariyar da suka bayar ta dogara ne da roko kotu ta yi watsi da hujjojin da…
Read More
‘Yan Arewa ba sa ƙiyayya da Kano

‘Yan Arewa ba sa ƙiyayya da Kano

Daga MUS'AB MAFARA (PHD) Wato wasu mutane sun ɗauka sharhin da a ke yi a Soshiyal midiya shi yake nuna matsayi da ra'ayin gama-garin al'umma a kan wani maudu'i da a ke tattaunawa a kai. Sannan wasu mutane kuma da zarar sun haɗu da maganar da ba ta yi mu su daɗi ba daga wasu mutune 'yan kaɗan, sai su yi wa al’ummar da mutanen nan suka fito kuɗin-goro cewa duka ra’ayinsu kenan. Kawai don ka ga, misali, kwamen 100 (in ma sun kai) na mutane da su ke sukar mutanen Kano ko su ke jin daɗin abun da ya…
Read More
Matasan marubuta ba sa son ana musu gyara – Mukhtar Ƙwalisa

Matasan marubuta ba sa son ana musu gyara – Mukhtar Ƙwalisa

"A rubutu na yi aure, na yi muhalli na kaina" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk wani tsohon makarancin littattafan Hausa, musamman littattafan labaran yaƙe-yaƙe da na barkwanci ba zai kasa sanin littattafan marubuci Mukhtar Ƙwalisa ba, wanda ya yi suna wajen tsara labarai masu ɗaukar hankali da sanya nishaɗi a zuciyar mai karatu. A wannan makon, shafin Adabi ya gayyato muku ɗan ƙwalisar marubuta, don jin abin da ya sa har yanzu yake ci gaba da wallafa littattafai duk kuwa da kasancewar takwarorinsa da dama yanzu harkar ta gagare su. A tattaunawar da suka yi da wakilin Blueprint Manhaja,…
Read More
Maulidi: Gwamna Lawal ya buƙaci Musulmi a dage da roƙa wa ƙasa zaman lafiya

Maulidi: Gwamna Lawal ya buƙaci Musulmi a dage da roƙa wa ƙasa zaman lafiya

Gwamnan Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi kira ga al'ummar musulmin jiharsa da ma ƙasa baki ɗaya da a ba da himma wajen roƙa wa Zamfara da ƙasa zaman lafiya. Ya yi wannan kira ne a cikin saƙon taya musulmi murnar bikin maulidin Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) da ya miƙa wa al'umma ta hannun kakakinsa, Sulaiman Bala Idris. A cewar Lawal, “Ina taya Muslmi ganin wannan rana ta 12 ga watan Rabi’ al-Awwal, rana mai albarka wadda a cikinta ne aka haifi Annabi Muhammad (SAW). “Yau rana ce mai matuƙar muhimmanci inda muke bikin haihuwar Annabi Muhammad (SAW)…
Read More
DSS ta cafke Editan Jaridar Al-Mizan, Ibrahim Musa

DSS ta cafke Editan Jaridar Al-Mizan, Ibrahim Musa

Jami'an DSS sun cafke Babban Editan Jaridar Al-Mizan, Malam Ibrahim Musa a Babban Filin Jirgin Saman Kano. Majiyarmu ta ce an kama Musa ne da safiyar ranar Laraba a hanyarsa ta zuwa Saudiyya don Hajjin Umara. Jaridar Al-Mizan mallakar Ƙungiyar Harkokin Musulunci ta Nijeriya (IMN) ce wadda aka fi sani da Shi’ia. Wata sanarwa da ta samu sa hannun Abdullahi Usman, ta ce 'yan uwan Musa sun yi kira da a sako shi ba tare da wani jinkiri ba. A cewar sanarwar, “Hukumomi ba su ba da dalilin kama Musa ba duk da dai cewa shi ɗin ɗan sahun gaba…
Read More