01
Oct
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban cocin Wisdom Church of Christ International, Prophet Bisi Olujobi, ya bayyana cewa, Ubangijinsa ya sanar da shi cewa, Gwamnan Jihar Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida), ya samu tagomashi a kotun sama, inda za ta rushe hukuncin baya na Kotun Zaɓen Gwamnan Jihar Kano na 2023, wacce ta sauke shi daga mulki kuma ta ɗora ɗan takarar gwamna na babbar jam’iyyar adawa a jihar, Nasiru Yusuf Gawuna. Prophet Olujobi ya bayyana hakan ne a a jiya Alhamis a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, yana mai cewa, hukuncin…
