Amfanin ayaba ga matan aure

Daga AISHA ASAS

Mai karatu sannunmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu taɓo ɓangaren ni’imar jikin mace da za a iya samu ta ɓangaren ayaba.

Na san wasu za su ga abin tamkar almara, kasancewar da yawa ba su ɗauke ta a matsayin komai ba face ƙwalama.

Sai dai ayaba kamar wasu daga cikin ‘ya’yan itace ‘yan’uwanta, tana taka muhimmiyar rawa a ƙarin ni’ima ga mata.

Ayaba na ɗaya daga cikin kayan qarin ni’ima na mata, yawan cinta, musamman idan kina haɗa ta da madara zai ba ki ni’ima dawamamma. Ga namiji kuwa, tana ƙara yawan maniyi. Sannan wannan haɗin na taimaka wa mai shayarwa, wurin samun ƙarin ruwan nono.

Ana niƙa ayaba da kankana (har bayan ta) tare da kanunfari kaɗan, a sha safe da dare don samun ƙarin ni’ima.

Idan ki ka samu minanas (garin, kuma kaɗan) ki ka haɗa shi da ayaba mai kyau, ki ka markaɗa, sai ki ka samu zuma mai kyau ta zama mahaɗin su, kina sha da dare kullum, gwargwadon hali, zai taimaka wurin magance matsalar bushewar gaba yayin auratayya (wannan haɗin ba shi da tasiri ga wadda ta ke da matsalar rashin sha’awa ko ciwon sanyi).

A vangaren mai ciki kuwa an so ta yawaita cin ayaba a lokacin da ta yi kusa haihuwa, domin tana hana bugun zuciya da mata masu juna biyu ke yi.