Ta yaya za a iya magance warin gaba

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Manhaja. A satin da ya gabata, mun tavo bayyani kan dalilan da ke haifar da warin gaban mace, wanda muka tabbatar ba halitta ba ce.

A wannan makon, da yardar mai dukka, za mu kawo wasu daga cikin ababen da uwar gida za ta yi don kawar da warin gaba, sai dai kamar yadda muka yi bayanin ababen da ke haifar da warin na gaba, zan so uwar gida ta fara da haddace su, ya zamana ta kauce wa dukka hanyoyin na samuwar warin kafin ta yi yunƙurin kawar da shi, dalili kuwa, ko kin magance shi yau, gobe zai iya dawowa, saboda ba ki bar abinda tun farko ke haddasa shi ba.

Ruwan zafi da kanunfari: dafaffen ruwan kanunfari na ɗaya daga cikin ababe masu sauƙi kuma masu saurin kawar da warin gaba.

Uwar gida za ta dafa kanunfarinta da ruwa mai tsafta, ta tarfa ɗan gishiri kaɗan a ruwan, idan ya dahu sosai, sai ta dinga tsarki da ruwan sau uku zuwa huɗu a rana, sai dai za ta dinga ɗumama ruwan lokaci-lokaci ko ta sa su a inda ba za su yi saurin hucewa ba, saboda ana so ta dinga tsarki da ruwan da zafinsu, sai dai ba irin wanda zai cutar da ita ba.

Kuma shi wannan haɗin ba iya warin gaba yake kawarwa ba, har ciwon sanyi da bai tsananta sosai ba.

Haɗin ganyen magarya: idan ki ka samu ganyen magarya, miski fari mai kyau, habbatu sauda, ganyen na’a-na’a, miyani da kuma anbu.

Ana haɗa su wuri guda, a dafa su sosai, sai a dinga zama na tsayin minti talatin safe da dare. Sai idan aka zo kwanciya a yi tsarkin ƙarshe da ruwan, amma masu ɗimi daga ruwan.

Haɗin kankana: ana amfani da busasshiyar kankana (bushewar da aka yi ba a rana ba), minanas, geron tsuntsaye, habbatu sauda, madara, ruwan kwakwa da kuma zuwa.

Za a dake busasshiyar kankana, a haɗa ta da habbatu sauda, geron tsuntsaye, minasas ha daɗa su da madara, a zuba ruwan kwakwa da kuma zuma, ana sha safe da dare.

Da yawa sun san wannan haɗi, kasancewar sa haɗi na ƙarin ni’ima, sai dai abinda ba su sani ba shi ne, tasirin sa ga kawar da warin gaba. Kenan magani biyu ne a lokaci guda a jikin mace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *