Ku ba wa iyalanku kariya daga cutar mashaƙo

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda yake haƙƙi da ya rataya kanka maigida na daga ci da sha ga iyalanka, haka ya kasance haƙƙi gare ka ka ba wa iyalanka kariya daga curutukan da ka iya yiwa iyalanka lahani.

Ba ma maigida kawai ba, a matsayinki ta uwa mai kula da sha’anin iyalinta ke ma ya kamata ki kula tare da mayar da hankali wurin ganin curutukan nan na zamani sun tsallake gidanki.

Wannan ne ya sa yake da matuƙar muhimmanci samun ilimi kan kowacce irin cuta da ke yaɗuwa, wanda hakan zai ba ku dama, wurin ba wa ‘ya’yanku da ma ku kanku kariya daga gare su. Kamar dai yadda masu iya magana suka ce, rigakafi ta fi magani.

Da wannan ne shafin Iyali na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ta zaƙulo ɗaya daga cikin cutuka masu illa ga jikin ɗan adam, wato cutar mashaƙo, don wayar da kan masu karatunmu, wanda muke fatan ya kasance tsani da za su taka don ba wa iyalansu kariya daga cutar. Kafin komai shin me ake cewa cutar mashaƙo?

Cutar mashaƙo wadda bature ke kura da diptheria, cuta ce da ke tava tsarin numfashin ɗan adam ta sanadiyyar majinar da ke lulluve saman fatar hanci ko maƙogaro, ta sanadiyyar hakan mai fama da ita ke samun wahalar yin numfashi.

Cuta ce da ba mu cika dauka da wani muhimmanci ba, sai dai tana da matuƙar hatsari, musamman ma ga yaranmu, duk da cewa, ba iya yara kawai ta tsaya ba, har manya na iya kamuwa da cutar ta mashaƙo, kuma idan ba a yi gaggawar ɗaukar mataki ba, za ta iya kashe yara cikin ƙanƙanin lokaci da kamuwarsu da ita.

Wannan cuta tana samuwa ne sanadiyyar wata ƙwayar cuta da ake kira da Corynebacterium diptheriae, kuma cuta ce da a wannan lokacin da muke ciki ta fara yawaita, kuma take yi wa yara ƙanana ɗauki ɗai-ɗai.

Ta yaya wannan cuta ta zama game gari?

Ita dai cutar mashaƙo ta fara yawaita ne sakamakon hanyoyin da ake iya samun ta, waɗanda suka haɗa da:

Ta hanyar haɗuwar iska: a sa’ilin da mai ɗauke da wannan cuta ta mashaƙo ya yi tari ko atishawa a kusa da wanda ba shi da ita, kuma tarin ko atishawar suka yi tasiri ta hanyar gauraya da iskan da shi ya shaƙa ba tare da shamaki ba, to akwai yiwa mai ƙarfi ta kamuwa da cutar a lokacin.

Amfani da kaya: idan ya kasance mai cutar ya yi amfani da wani abu kamar ƙyale, tawulin wanka, kayan sawa, da sauran kayan amfani na yau da kullum, sai wani ya yi amfani da shi, ta wannan hanyar ma za a iya kamuwa da cutar.

Haɗuwar jiki: yayin da cutar ta samu ga wani, yaro ko babba, to akan so a nisanta shi da sauran ‘yan’uwansa ta fuskar kwanciya, wasanni da sauran mu’amala ta gogayya da jiki. Musamman ma yara ƙana. Shi ya sa a duk gidan da wani yaro ya kamu da cutar mashaqo da ƙyar ya yi ya gama ba tare da ya samu aboki ba, matuƙar akwai yara a tare da shi.

Wannan na ɗaya daga cikin muhimmancin sanin cuta da yadda za a iya kaucewa samuwar ta ko yaɗuwarta musamman ma gare ki uwa, domin ke ce mai iya ba wa ‘ya’yanki kariya a ire-iren cutuka kamar ta mashaƙo, ta hanyar raraba masu mu’amala da kuma kayan amfani har sai ranar da ya samu lafiya, koda kuwa hakan na nufin raba wa yaran gida ne, har sai kin gama jinyar marar lafiya.

Haka ma a ɓangaren ke da maigida, idan wannan cutar ta samu ɗaya daga cikinku, to yana da kyau ku raba shimfiɗa na ɗan lokacin jinya, ku nisanci mu’amala ta haɗuwar jiki, ko kayan amfani zuwa lokacin da sauƙi zai samu.

Ta ya uwar gida za ta gane mijinta ko ɗanta na fama da cutar mashaƙo?

Akwai alamomi masu yawa da uwa za ta iya gani da za su iya bata haske kan cutar mashaƙo ta sami ɗaya daga cikin ahalinta.

Ita dai cutar mashaƙo ba ta ɗaukar dogon lokaci kafin ta bayyanar da kanta, kasancewar ba ta wuce kwanaki biyu zuwa uku za ta fara bayyana alamomi kamar haka; zazzavi, yawan jin sanyi, kumburin wuya, tari mai kaushi wanda ke bayyana majina na cikin abinda ya riƙe maƙoshi.

Akwai kuma wahala wurin iya haɗiye abinci, da kuma wahalar fitar da numfashi, ƙaiƙyayin maƙoshi, wayan gajiya, ciwan kai, da yawan tari, da kakin majina.

Da wannan ne shafin Iyali na jaridar Manhaja, ke kira da babbar murya ga iyaye musamman mata kan saka ido sosai tare da nisanta ‘ya’yansu da abinda zai iya zama silar kamuwarsu da cutar ta mashaqo. Idan kuwa har ƙaddara ta riga fata, a bi hanyoyi wurin ganin an samar masu da warakar cutar tare kuma da ba wa sauran yaran da ba su kamu da cutar ba kariya.

Daga ƙarshe ina so iyaye su sani, ita wannan cuta ta mashaƙo tana da allura ta rigakafi kamar curuta da dama, don haka yake da kyau ku yi ƙoƙarin ganin kun kai kanku da ‘ya’yanku an yi maku allurar ta rigakafin cutar mashaƙo don kuvutar da kanku da ‘ya’yanku daga wannan cuta mai hatsarin gaske.

Kamar yadda na faɗa a baya, rigakafi tabbas ya fi magani.