UAE ta ɗage haramcin bai wa ‘yan Nijeriya bisar shiga ƙasar

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Mohamed bin Zayed Al Nahyan, sun cimma yarjejeniyar ɗage haramcin bai wa matafiya daga Nijeriya bisa ta shiga ƙasar.

A ranar Litinin shugabannin biyu suka cimma wannan matsaya a Abu Dhabi, inda aka amince jiragen Etihad Airlines da na Emirates Airlines su ci gaba da zirga-zirga a Nijeriya nan take.

Kuma yarjejeniyar ci gaba da zirga-zirgar jiragen ba ta shafi gwamnatin Nijeriya ta biya wasu kuɗaɗe nan take ba.

La’akari da manufar Tinubu ta inganta tattalin arzikin Nijeriya haɗa da sauran tsare-tsaren bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da ya gabatar wa takwaran nasa, ya sa UAE ta amince ta zuba jari na biliyoyin Dala a Nijeriya.

Tinubu ya yaba da ƙawancen takwaran nasa na amincewa da su yauƙaƙa kayakkyawar dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu.