Juyin mulkin Burkina Faso: Reshe ya nemi juyawa da mujiya

Daga BASHIR ISAH

An cafke wasu manyan jami’an soji a ƙasar Burkina Faso bisa yunƙurin yin juyin mulki ga sojojin da suka hamɓarar da mulkin dimokraɗiyya a ƙasar.

Mai gabatar da ƙara na mulkin sojin ƙasar, Manjo Alphonse Zorma ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.

Ya ce a makon da ya gabata masu bincike suka samu rahoto kan shirin da wasu sojoji da tsoffin sojojin ƙasar ke yi na neman kifar da sosjojin da ke riƙe da ƙasar a halin yanzu.

Sanarwar ta ce cikin hasfsoshin da lamarin ya shafa har da Kyaftin Ibrahim Traore wanda jigo ne a sojin ƙasar.

An kama jami’an da hannu cikin yunƙurin juyin mulki da take dokar soji,” in ji Manjo Alphonse Zorma.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Windinmalegde Kabore da Brice Ismael Ramde da tsohon sojan ƙasar Sami Dah wanda a baya an same shi da laifin yi wa shugabancin ƙasar zagon ƙasa.