03
Sep
Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya a ranar Laraba, ta tabbatar da murƙushe haramtattun matatun mai a Imo da Delta, tare da kama wasu litar man da aka tace ba bisa ƙa'ida ba. Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja. Nwachukwu ya ce, dakarun sojojin na 343 Artillery Regiment, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, sun fatattaki wani sansanin ɓarayin mai da ke unguwar Obokofia a Imo yayin da suke gudanar da aikin satar mai. Ya ƙara da cewa, sojojin sun kuma kwato…
