Editor

9513 Posts
Ma’aikatar Shari’a na fama da rashin kuɗin biyan basukan shari’a

Ma’aikatar Shari’a na fama da rashin kuɗin biyan basukan shari’a

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babbar Lauyar Gwamnatin Tarayyar Nijeriya, Beatrice Jeddy-Agba, ta bayyana cewa, Ma’aikatar Shari’ar ba ta samun wani kaso na kasafin kuɗi ba, don biyan basussukan shari’un da take gudanarwa ba. Jeddy-Agba, wacce kuma ita ce babbar sakatariya a ma’aikatar ta shari’ar ƙasar, ta bayyana hakan a Abuja, Babban Birnin Tarayya, a wani taron tattaunawa kan samun hanyoyin magance take haƙƙin bil’adama a Nijeriya. Taron mai taken ''Tattauna dabarun samun hanyoyin magance take haqqin bil'adama a Nijeriya" an shirya shi ne a bayan fagen taron ƙungiyar lauyoyin Nijeriya, NBA, da ke gudana a Abuja. Jeddy-Agba, wadda Enoch Simon,…
Read More
Gwamnatin Kano ta sake naɗa sabbin mataimaka na musamman 57

Gwamnatin Kano ta sake naɗa sabbin mataimaka na musamman 57

DAGA IBRAHIM HAMISU a KANO Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sake amincewa da sake naɗa sabbin muƙamai da za su taimaka masa cikin ƙunshin gwamnatinsa a matakai daban-daban. Ta cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labaran na gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Juma'a ta ce Injiya Abba Kabir Yusuf ya amince waɗannan mutanen da za su taimaka masa a wuraren gudanar da ayyukan su kamar haka: Anas Abba Dala, Senior Special Assistant, Political Awareness Ali Muhammad Bichi, Senior Special Assistant, Religious Affairs Alhajiji Nagoda, Senior Special Assistant, Information Babban Alhaji Sagagi, Senior…
Read More
Shettima na da halayyen jagoranci, inji Sheriff

Shettima na da halayyen jagoranci, inji Sheriff

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon gwamnan Borno, Ali Sheriff, ya bayyana Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima a matsayin jagora wanda ke misalta muhimman manufofin jagoranci nagari. Sheriff ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai jim kaɗan bayan ya kai ziyarar nuna goyon baya ga Shettima a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Ya godewa shugaban qasa Bola Tinubu bisa samun Shettima wanda ya cancanci zama mataimakinsa. Sheriff ya ce, “Na zo nan ne domin ganin Mataimakin Shugaban Nijeriya, wanda ƙanena ne, wanda na yi aiki tare da shi sosai lokacin…
Read More
Yadda aka raba jaddawalin Gasar Zakarun Turai

Yadda aka raba jaddawalin Gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jaddawalin gasar cin Kofin Zakarun Turai: Man United na rukuni ɗaya da Bayern Munich, Madrid za ta fuskanci Napoli An kammala fitar da jadawlin gasar Zakarun Turai na bana, inda ƙungiyoyi guda 32 suka san rukunnen da suka faɗa kuma da ƙungiyoyin da za su fafata da su. Man United za su kara da Harry Kane bayan an haɗa su da zakarun Bundesliga yayin da Arsenal ta tashi kunnen doki. Manchester United ta yi kunnen doki sosai bayan dawowarta gasar zakarun Turai kuma za ta kara da Bayern Munich a rukunin A da kuma Copenhagen da…
Read More
Raɗɗa ya bada umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage raɗaɗin cire tallafin mai

Raɗɗa ya bada umarnin raba shinkafa buhu 40,000 don rage raɗaɗin cire tallafin mai

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Umar Dikko Raɗɗa ya bayyana cewar ya bada umarnin raba shinkafa buhu 40,000 nan take, ga al'ummar jihar da nufin rage raɗaɗin matsin rayuwa bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi. Bayanin rabon tallafin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ta sayo shinkafar ne daga kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da jihar ta karɓa daga gwamnatin tarayya.Ya kuma ce ya amince da kafa kwamitoci don raba shinkafar a matakan ƙananan hukumomi da mazaɓu…
Read More
APC ta musanta saka sunan Wike a kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamnan Bayelsa

APC ta musanta saka sunan Wike a kwamitin yaƙin neman zaɓen Gwamnan Bayelsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da jerin sunayen yaqin neman zaɓen da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Imo, Kogi, da Bayelsa. A wani saƙo da ya wallafa a dandalin X (wanda aka fi sani da Tiwita) a ranar Talata, Muhammad Argungu, sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC, ya ce Abdullahi Ganduje, shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya amince da kundin tsarin mulkin kwamitin yaqin neman zave tare da tuntuvar Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC). A cikin jerin sunayen da aka soke…
Read More
Nijar: ‘Yan Nijeriya mazauna iyaka na zargin jami’an tsaro suna muzguna musu

Nijar: ‘Yan Nijeriya mazauna iyaka na zargin jami’an tsaro suna muzguna musu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu mazauna unguwar Magamar Jibiya dake kan iyakar Nijeriya da Nijar a jihar Katsina, sun zargi jami'an tsaro da ɗaukar su kamar 'yan Nijar. Mutanen sun yi wannan zargin ne a wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Katsina ranar Talata. Sun yi iƙirarin cewa jami’an Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) da ba a san ko su waye ba ne ke tauye haƙƙinsu a kullum. A cewar Ɗayyabu Muhammad, jami’an tsaro da ke kan hanyar Katsina zuwa Jibiya a kodayaushe suna bin su a duk lokacin da suka ga suna…
Read More
Za mu haɗa kai da al’umma don magance matsalolin da sauyin yanayi ke jawowa – Ɗahiru Muhammad

Za mu haɗa kai da al’umma don magance matsalolin da sauyin yanayi ke jawowa – Ɗahiru Muhammad

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Dakta Ɗahiru Muhammad Hashim, Ko'odinetan Ayyuka na Jihar Kano (ACReSAL), ya bayyana cewa za su yi aiki da ya haɗa da wayar da kan al'umma, don magance matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa. Ya ce, aikinsu na haɗin gwiwa ne a tsakanin Majalisar Dankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da jihohi 19 na Arewa da Birnin tarayya Abuja. Ya bayyana haka ne da yake zantawa da 'yan jarida ciki har da wakilin Blueprint Manhaja, inda ya yi nuni da cewa babban aikin da ma'aikatar take shine na daƙile matsaloli da suka shafi zaizayar ƙasa da hana kwararowar…
Read More
Erdogan zai gana da Putin kan samar da hatsi a duniya

Erdogan zai gana da Putin kan samar da hatsi a duniya

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na shirin ziyartar Rasha domin tattaunawa da takwaransa na ƙasar, Vladimir Putin game da farfaɗo da yarjejeniyar fitar da hatsi daga tekun Black Sea. Ana sa ran tattaunawar tsakanin Erdogan da Putin ta yi armashi ta yadda za a iya amfani da ita wajen faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiyar Ukraine. Jam’iyyar Erdogan mai mulki ta shaida wa manema labarai cewa, za a gudanar da wannan tattaunawar ce a wurin shaƙatawa da ke gavar Tekun Black Sea a birnin Sochi, inda za su mayar da hankali kan kawar da matsalar ƙarancin abinci da ke tunkarowa. Watakila shugaba…
Read More
Sanata ya bai wa ƙungiyar manoma tirela biyu na taki a Kebbi

Sanata ya bai wa ƙungiyar manoma tirela biyu na taki a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa ya bai wa haɗaɗɗiyar ƙungiyar manoma ta jihar Kebbi tirela biyu na takin zamani. Da ya ke hannanta takin ga shugabannin ƙungiyar a madadin Sanatan, Alhaji Bara'u Abubakar Abdullahi ya bayyana cewa Sanata a ko da yaushe shirye ya ke da ya kawo duk wani abu na cigaba wanda al'umma za ta amfana da shi ba tare da nuna bambancin siyasa ba. Ya ƙara da cewa tallafawa al'umma ya zama wajibi ga duk wani ɗan ƙasa nagari da ke riƙe da wani matsayi musamman…
Read More