Editor

9513 Posts
APC a Zamfara ta nesanta kanta da zargin yunƙurin hamɓarar da Gwamna Dauda

APC a Zamfara ta nesanta kanta da zargin yunƙurin hamɓarar da Gwamna Dauda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar All Progressives Congress APC a Zamfara ta nesanta kanta daga zargin kitsa yunƙurin hamɓarar da Gwamna Dauda Lawal kamar yadda jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta yi zargi. Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan zargin da jam’iyyar PDP ta yi wa APC a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau. A cewar sanarwar, zargin da jam'iyyar PDP ta yi wani shiri ne da jam’iyyar ta PDP ke yi ta hanyar amfani da tsohon aminin Gwamna…
Read More
Juyin mulkin Gabon: Za mu mayar da martani tare da sauran shugabanni – Tinubu

Juyin mulkin Gabon: Za mu mayar da martani tare da sauran shugabanni – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana bin halin da ake ciki a Gabon "cikin damuwa" sakamakon juyin mulkin da sojoji suka sanar a ranar Laraba. Tinubu, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ya ce yana duba hanyoyin da zai mayar da martani tare da sauran shugabannin Afirka. Da yake ba da misali da juyin mulkin baya-bayan nan, Tinubu ya ce "annoba" ta kama Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana. A ranar Laraba sojoji a Gabon suka sanar da ƙwace mulki…
Read More
Shugabannin ƙwallon ƙafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus

Shugabannin ƙwallon ƙafar Sifaniya sun buƙaci Rubiales ya yi murabus

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na Sifaniya sun yi kira ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Luis Rubiales da ya gaggauta yin murabus bayan ya sumbaci 'yar wasa Jenni Hermoso. Rubiales, mai shekaru 46, ya sha suka sosai bayan da lamarin ya faru bayan kammala wasan ƙarshe na gasar kofin duniya na mata a da Sifaniya ta lashe. Hermoso, mai shekaru 33, ta ce ba ta amince da sumbar da Rubiales ya yi mata ba. Tun da farko, masu gabatar da ƙara na Sifaniya sun ƙaddamar da bincike na share fage kan ko lamarin ya kai wani…
Read More
Ɗumamar yanayi za ta fara laƙume rayuka a duniya – IMF

Ɗumamar yanayi za ta fara laƙume rayuka a duniya – IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa, matsalar ɗumamar yanayi na barazana ga matalautan ƙasashe, wanda idan har ba a ɗauki matakan gaggawa ba, za ta fara haifar da hasarar rayuka nan da shekarar 2060. IMF ya ce, za a samu ƙaruwar kaso 8.5 na adadin rayukan da za a yi asara, musamman a yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi, kuma kaso 14 na waɗannan ƙasashe za su fuskanci qaruwar tsananin zafi. Daga cikin ƙasashe 39, wanɗanda ke ɗauke da kusan mutane biliyan guda na al’ummar duniya, rabi daga cikinsu da ke fama da wannan…
Read More
Matar da har yau ban san ta ba ce ta koya min yadda zan gyara rubutuna – Zee Kumurya

Matar da har yau ban san ta ba ce ta koya min yadda zan gyara rubutuna – Zee Kumurya

"Rashin haɗin kan marubta onlayin ne ya fi damuna" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A wannan makon muna ɗauke ne da tattaunawar da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi da marubuciya Zainab Shehu Abdullahi, wacce aka fi sani da Zee Kumurya. A cikin tattaunawar tasu za ku ji yadda ta fara samun kanta a harkar rubutun adabi, da buƙatarta na ganin an samu haɗin kai da kyakkyawan jagoranci a tsakanin marubuta. A yi karatu lafiya. MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki? ZEE KUMURYA: To, Alhamdulillahi. Cikakken sunana shi ne Zainab Shehu Abdullahi, wacce aka fi sani da…
Read More
Kafar sadarwa na taimakon mata matuƙa ta fuskar kasuwanci – Maryam Ango

Kafar sadarwa na taimakon mata matuƙa ta fuskar kasuwanci – Maryam Ango

"Da wuya kaga an wulaqanta macen da ke da ilimi da aiki da shi" Daga AISHA ASAS A yau shafin Gimbiya na jaridarku mai farin jini, Manhaja, ya zaƙulo maku ɗaya daga cikin mata matasan da suka canza kallon da ake yi wa mata ta ɓangaren sana'a, yayin da suka yi zurfin tunani wurin amfani da zamani wurin neman na kai. Sanannen abu ne kafafen sada zumunta sun zama wata taba ga matasa ta yadda za ka samu kaso mai yawa daga cikinsu da ba za su iya wuni ba tare da sun leƙa ba. Da yawa sanadiyyar soyayyarsu da…
Read More
Juyin mulki: Sojoji sun naɗa Kanal Brice Nguema a matsayin sabon shugaban Ƙasar Gabon

Juyin mulki: Sojoji sun naɗa Kanal Brice Nguema a matsayin sabon shugaban Ƙasar Gabon

Sojojin da suka yi juyin mulki a ƙasar Gabon sun sanar cewa Kanal Brice Clotaire Oligui Nguema ne sabon shugaban ƙasar wanda hakan ya kawo ƙarshen mulki na shekara 55 da zuri'ar Bongo suka shafe suna yi a ƙasar. Manhaja ta rawaito a ranar Laraba sojojin ƙasar suka hamɓarar da Ali Bongo Ondimba daga karagar mulki tare da soke zaɓen da aka ce Odimba ne ya lashe. Sun ce zaɓen da ya gudana a ƙasar cike yake da maguɗi. A ranar Talata da daddare Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta bada sanarwar sakamakon zaɓen inda Ali Bongo ya samu ƙuri'u kashi…
Read More
Darasin da za mu koya daga shirin Mata A Yau na tashar Arewa 24

Darasin da za mu koya daga shirin Mata A Yau na tashar Arewa 24

'Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU'Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Shafukan sada zumunta, musamman manhajar Facebook da WhatsApp sun cika da muhawara da rubuce-rubuce game da wasu kalamai da ake danganta su da shirin nan na Mata A Yau da tashar talabijin ta Arewa 24 ke gabatarwa, wanda ke tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar mata da ta iyali. Jama'a da dama sun yi ta bayyana ra'ayoyi mabambanta game da zargin da suke yi na cewa, manufofin shirin suna karo da koyarwar addinin Musulunci, da al'adar al'ummar Arewa. Haka kuma yadda masu gabatar da shirin suke zaƙewa wajen bayyana rashin dacewar wasu abubuwa…
Read More
Tallafin Biliyan 5 ga jihohi: Shawara zuwa ga gwamnatin jihar Sakkwato

Tallafin Biliyan 5 ga jihohi: Shawara zuwa ga gwamnatin jihar Sakkwato

Daga YAHAYA ABUBAKAR DOGON DAJI Zuwa ga mai girma gwamnan jihar Sokoto. Fatan saƙona ya same ka cikin Aisha lafiya. Don Allah ina ba da shawara game da yadda za a yi amfani da kuɗin tallafin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya za ta raba ko ta raba wa jihohi 36 da suke a Nijeriya. Shawarata ita ce, Naira biliyan 5 ɗin nan a raya Kamfanin sufuri mallakin gwamnati jihar Sokoto (Sokoto State Transport Authority). Wannan Kamfani yana da matuƙar amfani ga dukkan mutanen Jahar Sakkwato. Biliyan 5 din nan a taƙaice za su iya samar wa Sakkwato irin waɗannan…
Read More
Sojoji sun karɓe mulki a Gabon

Sojoji sun karɓe mulki a Gabon

Sojojin ƙasar Gabon sun sanar da ƙwace iko daga gwamnati mai ci tare da rushe sakamakon zaɓen da aka bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe. Kafin sanarwar sojojin, bayanai sun ce an shafe tsawon sa’o’i ana jin ƙarar harbin bindiga a sassan Libreville babban birnin ƙasar kodayake babu tabbacin ko musayar wuta ce ko kuma kawai sojojin na harbin iska ne. Cikin jawabin kai tsayen da suka yi ta gidan talabijin ɗin ƙasar da safiyar Laraba, sojojin sun sanar da rushe dukkanin sassan gwamnati ciki har da majalisun dokoki da kuma kotun kundin tsarin mulki. A cewar…
Read More