APC a Zamfara ta nesanta kanta da zargin yunƙurin hamɓarar da Gwamna Dauda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress APC a Zamfara ta nesanta kanta daga zargin kitsa yunƙurin hamɓarar da Gwamna Dauda Lawal kamar yadda jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta yi zargi.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan zargin da jam’iyyar PDP ta yi wa APC a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Gusau.

A cewar sanarwar, zargin da jam’iyyar PDP ta yi wani shiri ne da jam’iyyar ta PDP ke yi ta hanyar amfani da tsohon aminin Gwamna Dauda Lawal Dare da ya saki wani sautin vata suna ga jam’iyyar APC da jagororinta.

Jam’iyyar ta ƙalubalanci cewa Anas Sani Anka ba mamban APC ba ne kuma baya goyon bayan jam’iyyar APC ta kowace fuska, kuma bai taɓa riƙe muƙaman siyasa a ƙarƙashin gwamnatin APC ba, don haka ba zai iya magana a madadin jam’iyyar APC a jihar ba.

Jam’iyyar ta kuma musanta faifan sautin da shi Anas Sani Anka ya fitar cewar Sanata Abdulaziz Yari ya ba shi kuɗaɗe don bai wa ‘yan majalisar jihar don su tsige gwamna Dauda Lawal tare da cewar Sanata Abdulaziz Yari yana ƙasar waje kuma bai da masaniya a kan hakan.

Jam’iyyar APC ta buƙaci dukkanin jami’an tsaro da abin ya shafa a qasar nan da su bankaɗo duk waɗanda suka aikata wannan aika-aika ciki har da wanda ya yi wannan faifan tunda duk tare da shi Anas Anka suka yi domin a hukunta su.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga magoya bayan ta a jihar da su kwantar da hankulan su ba tare da kawo rashin zaman lafiya ba a jihar.