Juyin mulkin Gabon: Za mu mayar da martani tare da sauran shugabanni – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana bin halin da ake ciki a Gabon “cikin damuwa” sakamakon juyin mulkin da sojoji suka sanar a ranar Laraba.

Tinubu, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ya ce yana duba hanyoyin da zai mayar da martani tare da sauran shugabannin Afirka.

Da yake ba da misali da juyin mulkin baya-bayan nan, Tinubu ya ce “annoba” ta kama Afirka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya bayyana.

A ranar Laraba sojoji a Gabon suka sanar da ƙwace mulki kuma suka yi wa Shugaba Ali Bongo mai shekara 64 ɗaurin talala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *