Darasin da za mu koya daga shirin Mata A Yau na tashar Arewa 24

‘Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU’Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Shafukan sada zumunta, musamman manhajar Facebook da WhatsApp sun cika da muhawara da rubuce-rubuce game da wasu kalamai da ake danganta su da shirin nan na Mata A Yau da tashar talabijin ta Arewa 24 ke gabatarwa, wanda ke tattauna matsalolin da suka shafi rayuwar mata da ta iyali. Jama’a da dama sun yi ta bayyana ra’ayoyi mabambanta game da zargin da suke yi na cewa, manufofin shirin suna karo da koyarwar addinin Musulunci, da al’adar al’ummar Arewa.

Haka kuma yadda masu gabatar da shirin suke zaƙewa wajen bayyana rashin dacewar wasu abubuwa da suka shafi kare mutuncin mata da shawarwarin su na neman kawo gyara, ba su dace da zamantakewar Malam Bahaushe ba, wanda wasu ma ke ganin sun yi hannun riga da koyarwar addini. Har ma da masu faɗar maganganu na aibatawa da cin zarafi ga masu gabatar da shirin, suna musu zargin ana amfani da su ne don ya qi da addini ko rusa tsarin auratayya baki ɗaya. Waɗannan zarge-zarge sun yi muni ainun, duba da kasancewar su mata musulmi, iyaye, kuma ’yan uwa a gare mu. Sannan a matsayin su na ’yan adam, suna iya yin kuskure a wani wuri, kuma akwai hanyoyi daban-daban na yin gyara ba sai an kai ga cin mutunci ba. 

Kodayake tashar Arewa 24 na da ’yancin fitowa ta kare kanta, ko ta yi magana don daidaita tsakaninta da masu kallonta, ko al’ummar da suke gabatar da shirye-shiryensu gare su. Hakan ba zai hana mu yin sharhi ko tsokaci game da abubuwan da suka faru ba, don ƙara faɗakar da jama’a, da samar da fahimtar juna.

Duk da yake a ta bakin ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin Halima Ben Omar, su a karan kansu suna ta ƙoƙarin ganawa da malamai da masu faɗa a ji, domin samun fahimtar juna da fayyace abubuwan da shirin yake faɗakarwa a kai, don a daina musu gurguwar fahimta. Kuma in sha Allahu nan gaba zan yi ƙoƙarin tattaunawa da wasu daga cikinsu, don kawo muku sakamakon abubuwan da suka biyo baya, daga ɓangarensu. 

Sai dai kafin lokacin zan so mu fahimci cewa, kowacce kafar watsa labarai na da manufofi da dalilan da ya sa ake kafata ko watsa shirye-shiryen ta. Sannan kafin a fara kowanne shiri sai hukumomin da abin ya shafa sun tantance su, sun kuma tabbatar da tsarin ayyukansu bai ci karo da dokokin ƙasa ko tsarin mulkin Nijeriya ba, wanda a cikinsa an tsare mutuncin kowanne addini da al’ada.

Kodayake tun bayan fitowar tashar a shekarar 2014 ’yan Nijeriya da dama sun riƙa nuna shakku da kokwanto kan manufofin kafuwar tashar mai amfani da harshen Hausa tsawon awa 24, musamman jin cewa tana da alaƙa da ƙasar Amurka. An yi ta zarge-zarge kan cewa tashar na kawo shirye-shirye masu gurvata al’adu da tarbiyya, musamman shirin nan na waƙe-waƙen hip hop wanda Aminu Abba Umar Nomis Gee ke gabatarwa, wato Top 10, da wasu shirye-shirye da suka shafi wasan kwaikwayo na Daxin Kowa, Manyan Mata, da kuma shi wannan shiri na Mata A Yau. 

Zan so in taƙaita bayanai na kan shirin Mata A Yau, wanda a kansa ne wannan dambarwa ta taso, kuma kamar yadda wani fitaccen marubuci, ɗan kishin Arewa, kuma mai faɗa a ji a harkokin cigaban al’umma, Dr Aliyu Tilde ya rubuta a shafinsa na Facebook, “Wannan yana daga shirye-shirye masu amfani ga al’umma, inda mata suke tattauna matsalolinsu kuma suke kiran ƙwararru don ƙarin haske. Na kan kalla, kuma na kan ƙaru sau da yawa.”

Nima zan iya cewa, ina kallon shirin Mata A Yau, kuma ina bibiyar yadda suke gabatar da tsarin shirin, duk da kasancewar ina da bambancin ra’ayi da su a wasu vangarori. Amma wannan ba zai hana in bayyana muhimmancin shirin ga rayuwar mata ba, da kuma kyakkyawan tsarin da aka yi wajen gina tsarin gabatar da shirin. Lura da yanayin bambancin shekaru da gogewar matan da ke gabatar da shirin, kowacce da vangaren da ta fito da kuma gungun matan da take wakilta. Don haka haɗin gambizar matan da suke gabatar da shirin, shi ma wani abu ne muhimmi, da yake nuna manufar shirin.

Sai dai duk da ƙoƙarin da tashar ke yi wajen kiyaye koyarwar addini da al’ada, ba a rasa wani lokaci da akan samu kurakurai a wasu maganganu da akan yi amfani da su. Wannan kuma dole ne mu yi musu uzuri kasancewar duk ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Kamar lafazin da ake ƙorafin ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin Aisha Umar Jajere ta yi amfani da shi, inda ta nuna cewa idan mata ba ta gaishe da mijinta ba, shi me zai hana ya gaisheta! Wannan a ra’ayin wasu masu tsokaci da kallon shirin ya savawa tarbiyya da zamantakewar auren Bahaushe, kuma yanayin kalaman nata za su iya sa mata su riqa raina mazajensu.

Kodayake na san ba hakan ne manufarta ba, sai dai ƙoƙarin kawo maslaha tsakanin waɗannan ma’aurata da aka ce maigidan ya aika da ƙorafi a kan matarsa ba ta gaishe shi. Kuma ko nima na goyi bayan ra’ayinta, don bai kamata rashin gaisuwa ya kawo savani ba, musamman tunda ma’auratan suna zaune lafiya da juna.

A irin zamantakewa ta yanzu ba duka iyali ne suke gaisuwa tsakanin miji da mata ba, gara ma dai tsakanin ’ya’ya da iyayensu ko yayye da ƙannai. Wannan ba yana nuna yin gaisuwa tsakanin ma’aurata ba shi da kyau ba ne, tarbiyya ce mai kyau, amma matasan yanzu na ganin kwana ɗaki ɗaya ko gado xaya ya ɗauke wannan buƙatar gaisuwar, musamman saboda ganin ana tare kowanne lokaci. Wannan na faruwa ne a irin yanayin da zamani ya kawo na canji a halin zamantakewa da ake fuskanta, a kowanne ɓangaren rayuwa. Dole ne a daidai wannan gaɓa a riƙa samun akasi, saboda sauyin da yake shigowa.

Hajiya Aishatu Giɗaɗo Idris wata fitacciyar marubuciya kuma mai ba da shawarwari kan zamantakewar iyali ta rubuta cewa, dole ne a ƙoƙarin daidaita jiya da yau a zamantakewar rayuwa sai an fuskanci turjiya da ƙalubale daga al’umma. Wannan haka yake ko a tarihin duniya, duk lokacin da wani sabon tunani ya zo ya ci karo da tsohon tsari, sakamakon ba ya kyau, a wani lokaci ma har asarar rai ake yi da dukiya, saboda nuna bore daga jama’a. Kamar yadda yanzu abubuwan da suka biyo bayan wannan shiri ya xaga hankalin masu gabatar da shirin, iyalinsu, mutuncinsu da mu’amalarsu da jama’a, sakamakon yadda aka kasa fahimtar su da mummunar fassarar da ake musu.

A cikin lafazi mai nuna ɗacin rai, “Hajiya Halima Ben Omar ta ce, shirin Mata A Yau bai tava kawo wata fatawa ko shawara da ta soki koyarwar addinin Musulunci ba, amma muna ƙoƙarin ganin an samu canji ga wasu abubuwa da al’ada ce ta kawo su ba addini ba. Sai dai abin mamaki wasu da ko kallon shirin ba su tava yi ba, sun bi duniya suna yaɗa cewa ana faxa da koyarwar addini.”

Lallai ne ya kamata wannan ya zama darasi gare mu duka, musamman tashar Arewa 24 da masu shirin Mata A Yau, su sani ana hallare da su, kuma kurar su ta riga da ta yi kuka tuntuni, don haka abu kaɗan ne za su yi ya zama matsala. Ya kamata su ƙara hattara da taka-tsantsan, kuma su riƙa tauna kalamansu suna sanya hikima cikin faɗakarwar da suke yi.

Sannan a ƙoƙarinsu na ganin sun kawo sauyi da cigaban rayuwar mata su riƙa fahimtar yanayin al’ummar da suke ciki, tsaurinta kan sha’anin addini da al’ada, da yadda canji ke wuyar samuwa a rayuwar Malam Bahaushe. Haka kuma su riqa tuntuɓar malamai a kai-a kai ana samun fahimtar juna da ƙarin haske kan wasu batutuwan da suke so su bijiro da shi. Na san shirin yana cike da ƙwararru, ’yan boko da malamai. Lallai a qara sa ido sosai! 

Ya zama wajibi shugabannin tashar Arewa 24 su tashi tsaye wajen ganin sun yi wa kansu gyaran fuska, sun haɗa kai da malamai da masu faɗa a ji don kyautata yadda jama’a ke yi musu kallon jakadun yahudawa, masu yaƙi da addini da gurɓata tarbiyya. Su kuma samar da wasu shirye-shirye da jama’a za su gamsu da su cewa, mummunan zaton da ake yi musu ba gaskiya ba ne.

Gare mu masu kallo, yana da kyau mu fahimci cewa kowacce tashar talabijin ko rediyo akwai manufar kafata, kamar yadda na bayyana a farko. Ba zai yiwu kowacce tasha ta zama kamar Sunnah TV ko NTA ba. Akasari tashoshin talabijin na zamani sun fi mayar da hankali ne kan faɗakarwa da nishaɗantarwa.

Shi ya sa ko a Arewa 24 ɓangaren nishaɗi ke da muhimmanci, domin da shi ne ake ɗaukar hankalin matasa ta yadda manufofin tashar na yaƙi da tsattsauran ra’ayin addini, cin zarafin mata, da shugabanci nagari, za su samu shiga zukatan matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *