Tallafin Biliyan 5 ga jihohi: Shawara zuwa ga gwamnatin jihar Sakkwato

Daga YAHAYA ABUBAKAR DOGON DAJI

Zuwa ga mai girma gwamnan jihar Sokoto. Fatan saƙona ya same ka cikin Aisha lafiya. Don Allah ina ba da shawara game da yadda za a yi amfani da kuɗin tallafin Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya za ta raba ko ta raba wa jihohi 36 da suke a Nijeriya.

Shawarata ita ce, Naira biliyan 5 ɗin nan a raya Kamfanin sufuri mallakin gwamnati jihar Sokoto (Sokoto State Transport Authority).

Wannan Kamfani yana da matuƙar amfani ga dukkan mutanen Jahar Sakkwato.

Biliyan 5 din nan a taƙaice za su iya samar wa Sakkwato irin waɗannan motocin na zamani har guda 250 zuwa 300.

Motocin suna da ƙarko sosai domin suna iya yin aƙalla shekaru 10 ba su mutu ba.

Wannan zai zama babbar rahama ga Sakkwatawan Shehu da sauran mazauna Sakkwato da ma baƙin dake shigowa suna fita.

Bugu da ƙari, motocin za su samar da damarmkin ayyukan yi ga Sakkwatawan Shehu. Za su kuma ƙara wa Jahar Sakkwato samun kuɗaɗen haraji, kuma ga babbar ribar da motocin za su tara wa gwamnati.

Motar za ta iya yi Naira miliyan 15 zuwa miliyan 20 har ‘yan kwangila, har yi mata dashe na (CNG ).

Shawarata shi ne, don Allah idan har an aminta za a siyo wazannan motoci ɗin, to don Allah a sayi na Kamfaninmu na nan gida Nijeriya wato (INNOSON MOYORS). Ba saboda komai ba sai don a yi wa kamfanoninmu na gida ciniki su ma su rabauta. Kuma kasuwanci ne mai kyan gaske.

Dalilin da ya sa na ba wannan shawarar shi ne, idan ba ku manta ba, tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya raba wa gwamnoni maqudan biliyoyin kuɗaɗe na (Paris Club Refund). Amma har yau ba wanda ya san inda gwamnoninmu saka kai kuɗaɗen.

Haka zalika, lokacin annobar Kurona (covid-19). Gwamnatin tarayya da Bankin Duniya sun raba wa jihohinmu maqudan kuɗaɗe da abinci a wannan lokacin da talakawan Najeriya suke cikin tsananin buqatar taimako, amma wallahi ma fi yawan gwamnonin Nijeriya ba su raba wa talakawa wannan tallafi (Palliatives) ɗin ba. Sauran kayan abincin ma lalacewa suka yi a wuraren da ake ɓoye kayayyakin Gwamnati.

Tunanin kar irin wannan varna ko ince zalunci ya sa na yi wannan rubutu a matsayin tawa shawara ga Gwamnanmu na jihar Sakkwato.

Don Allah a ɗauki wannan shawarar tawa a yi amfani da ita.

Yahaya Dogondaji, mai sharhi ne da nazari kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *