Editor

9513 Posts
Wanda ya zana tutar Nijeriya, Pa Taiwo Akinkunmi ya kwanta dama

Wanda ya zana tutar Nijeriya, Pa Taiwo Akinkunmi ya kwanta dama

A wannan Laraba aka sanar da rasuwar Pa Akinkunmi wanda ya zana tutar Nijeriya mai ɗauke da launin fari da kore. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 87. Ɗan marigayin mai suna Samuel Akinkunmi me ya sanar da rasuwar mahaifin masa a shafinsa na Facebook. Pa Akinwumi ɗan asalin Owu ne a Abeokuta, Jihar Ogun, wanda aka haife shi a ranar 10 ga Mayun 1936. A halin rayuwarsa, marigayin ya yi karatu a gida da kuma ƙetare. A ranar samun 'yancin kan ƙasa, wato 1 ga Oktoban 1960, aka ɗaga tutar Akinkunmi ya tsara a madadin ta turawan mulkin…
Read More
Tsakanin ECOWAS da Nijar: Abubuwa 7 da ya kamata mu sani

Tsakanin ECOWAS da Nijar: Abubuwa 7 da ya kamata mu sani

Ba 'yan Arewa ne kawai ba sa son yaƙi da Nijar ba, Yan kudancin Najeriya na adawa da shiga yaƙin kuma suna amfani da shafukan da suka fi tasiri irin Twitter, Tiktok da jaridu wajen bayyana haka. Sai dai damuwarsu ba ta taƙaita a zumuntar Nijeriya da Nijar ba, akasarin sun fi damuwa da ganin Rasha da Faransa ne za su yi amfani da 'yan Afirka su yaƙi junansu a madadin muradunsu. Don haka, kada garin ƙoƙarin raya zumuncinmu da Nijar mu haifar da ƙabilanci a cikin gida. Ƙoƙarin korar wata ƙasar Turai da gayyato wata da ƙasashen yammacin Afirka…
Read More
Juyin mulki a yammacin Afirka

Juyin mulki a yammacin Afirka

Daga AMINU KANO Juyin mulki, irin wanda sojoji ke kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin farar hula domin jan ragamar shugabancin ƙasa, ba sabon abu ba ne a tarihin siyasar ƙasashen duniya, ciki har da na Nahiyar Afirka. Hakan na nufin, har a ƙasashen da ke wajen nahiyar Afirka, sojoji sun sha amshe ragamar mulkin ƙasa daga hannun shuwagabannin fararen hula. Sai dai, matsalar juyin mulki ta fi zama ruwan dare a yankin Afirka ta Yamma (West Afirka). Ma fi yawancin qasashen da ke wannan yanki sun samu 'yanci ne daga mulkin mallakar ƙasashen Turai irinsu Birtaniya da Faransa daga 1957 zuwa…
Read More
Ku mara wa gwamnatin Tinubu baya, kiran Ministan Labarai ga gwamnoni

Ku mara wa gwamnatin Tinubu baya, kiran Ministan Labarai ga gwamnoni

Daga BASHIR ISAH Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan 'Yan Ƙasa, Mohammed Idris Malagi, ya yi kira ga gwamnoni da su mara wa ƙudurori takwas na Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya, yana mai cewa burin ƙudurorin ne janyo wa Nijeriya martabawa a tsakanin ƙasashen duniya. Malagi ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin Gwamnan Neja, Mohammed Umar Bago, a ofishinsa da ke Abuja a ranar Talata. Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a yayata ƙudurorin gwamnatinsa don amfanin 'yan ƙasa, ya ce Tinubu na sane da tsananin da 'yan ƙasa ke fuskanta sakamakon koma…
Read More
NNPP ta dakatar da Kwankwaso bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

NNPP ta dakatar da Kwankwaso bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Kwamitin Amintattu (BoT) na Jam'iyyar NNPP ya dakatar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar a babban zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon-ƙasa. Kazalika, Kwamitin (BoT) ya dakatar da Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam'iyyar. Har wa yau, Kwamitin ya naɗa shugabannin jam'iyyar a matakin ƙasa ƙarƙashin jagorancin Dr Agbo Major a matsayin shugaban riƙo na ƙasa da kuma Mr Ogini Olaposi a matsayin muƙaddashin Sakatsren jam'iyya na ƙasa tare da wasu mutum 18. Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewar, dakatarwar ta wata shida ne. Majiyarmu ta ce an cim…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin haɓaka fannin ƙirƙira 

Gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin haɓaka fannin ƙirƙira 

Daga AISHA ASAS  Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi alƙawarin sabunta fannin ƙirƙira a ƙoƙarin ganin sunan Nijeriya ya fita a matsayin babban birnin da damfara ta yada zango. Sabuwar Ministar Raya Al’adu da Inganta Tattalin Arziki, Hannatu Musawa ce ta yi wannan jawabi a lokacin da ta kai ziyara mafaifarta, Jihar Katsina, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata. Hannatu ta bayyana cewa, za a yi dukkan mai yiwa don ganin an goge ƙaurin suna da Nijeriya ta yi, na zama babbar ƙasa a duniya da ta fi yawaitar masu damfara. “Za mu mayar da…
Read More
Gwamnatin Kano ta rage kuɗin manyan makarantu da kaso 50%

Gwamnatin Kano ta rage kuɗin manyan makarantu da kaso 50%

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta rage wa ɗalibai 'yan asalin jihar da ke karatu a makarantun gaba da sakandare kuɗin makaranta da kaso 50%. Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar, Dr. Yusuf Ƙofar Mata ne ya sanar da haka a ranar Litinin, yayin da ya ke ganawa da manema labarai. Ƙofar Mata ya ce, gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin ta rage wa iyaye raɗaɗin biyan kuɗin makaranta sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, sakamakon cire tallafin man fetur. Ya kuma ce ragen kuɗin makarantar ya shafi ɗaukacin ɗalibai da ke karatu a manyan…
Read More
Mahaifiyar Mawaƙi Wizkid ta zama riga mu gidan gaskiya

Mahaifiyar Mawaƙi Wizkid ta zama riga mu gidan gaskiya

Daga AISHA ASAS  Shahararren mawaƙin da tauraruwarsa ke haskawa a wannan zamani, Ayodeji Ibrahim Balogun, wanda aka fi sani da Wizkid, ya yi babban rashi, inda mutuwa ta ɗauke mahaifiyarsa mai suna Misis Jane Dolapo. An ruwaito cewa, Misis Balogun ta mutu ne a ranar Juma'a, sai dai har zuwa yanzu babu wani cikakken bayanin abinda ya yi sanadin ajalinta. Sannan ba a ji komai daga bakin ɗan nata mawaƙi Wizkid ba. Watakila hakan ba ya rasa nasaba da zamewarta ginshiƙi ga rayuwarsa, domin ta ba shi goyon baya, kuma ta kasance ƙwarin gwiwa gare shi akan harkar waƙan da…
Read More
Jaruma Hannatu Umar Sani ta rasu

Jaruma Hannatu Umar Sani ta rasu

Daga AISHA ASAS  A ranar Lahadin ta makon iiya, 20 ga watan Agusta, masana'antar Kannywood ta tashi da wani sabon rashi. Duk da cewa ta rasa ɗaya daga cikin tsofaffin jarumanta ne, hakan bai hana mutuwar ta zama abin alhini gare su da kuma masoyanta ba, sakamakon irin rawar da ta taka a lokacin da take masana'antar.  Jaruma Hannatu Umar ta amsa kiran mahalicci a gidan yayarta da ke unguwar Katampe a Birnin Tarayya, Abuja, kamar yadda Mujallar Fim ta ruwaito.  Wani abin tava zuciya da mutuwar jarumar shi ne, ba ta tare da wata rashin lafiya bare har a…
Read More
Gudunmawar sarakunan Nijar wajen bunƙasa al’adu da zaman lafiya

Gudunmawar sarakunan Nijar wajen bunƙasa al’adu da zaman lafiya

Daga WAKILINMU Babu shakka masarautun ƙasar Nijar kaffatanninsu masarautu ne masu cike da haiba da kuma ɗimbin tarihi kuma masu adalci ga al'ummar da suke shugabanta. Duk mutumin da ya kasance mai bibiyar tarihi zai yarda kuma har ma ya aminta cewa sarakunan ƙasar Nijar ba su da kyashi ko baiken jin cewa sun taimake ka wajen samar da tarihi da kuma labarin da abin da ya shafe su, kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba kamar yadda hausawa ke azancin magana da cewa wai ‘Gani Ya Kori Ji’. Bari na fara da Masarautar Sultan ta Damagaran a shekarar…
Read More